Ajiyen kudi domin tufafin nan

Koyan yadda zaki ajiyen kudin ki

Ina tafiya daga makaranta wata rana sai naga wani tufafi mai kyau a wani bangaren titin. Bayan na gama kallon tufafin na minti biyar, na yanke shawara na shiga shagon na tambaye mutanen farashin.

“Dubu goma”, mai shagon tayi ihu. Ta kale ni tayi tunani, “ya zan iya daurewa na siya wannan tufafin?” Amma bayan wata daya, na koma shagon na siya tufafin. Kuna son ku san yadda nayi? Bara na baku labari.

Abun farko dana fara yi shine na tambaye kaina “ Ya zan samu kudin?” Sai na rubuta dukka yadda zan iya samun kudi.

  • Kudin kashewa daga iyaye na.
  • Kudi daga dan uwar mahaifi na ko yar uwar mahaifiya ta
  • Taimakon makwafci na ko abokan iyali na wanke kayan su, ko motan su, ko tsaftace gidan su.
  • Siyar da kayan wasa na da bana bukata kuma. Harda kayan sanyawa na da bane iya sanyawa kuma

Bayan na gama rubuta dukka, na rubuta yadda zan ajiyen dubu gomar (10,000). Wadannan abubuwan ne nayi da suka taimake ni

  • Na rubuta duk kudin dana samu a cikin a wani littafi
  • sai na rubuta yadda zan ajiya daga kudin
  • Na cire ajiya na tukun daga cikin kudin dana samu
  • Sai na rubuta dukka abubuwan da nake son na siya, sai na cire wanda bana bukata
  • Na bawa kai na wata daya na ajiyen kudin sai na rubuta a takada na.
  • Ban bawa mahaifiya ta kudin ba. Na gina asusun da na ajiye kudin.

Wadannan ne abubuwan da nayi domin na samu tufafin nan. Kema zaki iya, Idan kina son ki siya abu kuma baki da isashshen kudi. Akwai wani abu da kike ajiyen kudi wa yanzu? Gaya mana shafin sharhin mu.

Share your feedback