Yan mata ne ke mulka duniya kuma kema zaki iya
Kin san mai yafi yin mafarki akan aikin da zaki yi nan gaba? Yin mafarkin da kuma koyan yadda zaki zama babban shugaba. Kasancewa da ikon tafiyad da wani masana’anta ba sauki, shiyasa bai yi wuri ki fara tsara abun da zaki yi tun Yanzu. Duk matakin da kika dauka Yanzu zai tura ki zama babban shugaba wata rana.
Ga wasu abubuwa da zai shirya ki a hanyar gaskiya:
Idan kina nan da iyalen ki da kuma abokan ki, kiyi kokari kada kiyi dukka surutun. Ki saurare su kuma ki tambaye su yadda suke yin sa. Idan suka rarraba wani matsalar su dake, kiyi iya kokarin ki ki samo wani maslaha. Dukka wannan zai yi taimako idan ke babban shugaba ce.
Bayan kin tsoma hannu cikin wani aiki, kada ki zama mutumin nan dake son ya kwsahe dukka yabo. Ki tabbata kowa ya samu yabo ma. Kiyi musu godiya da suka taimake ki cin nasara da aikin. Ba zai nuna kawai wai kina da tabbas, amma zai nuna cewa kina da kula. Tun da wuri ki koya yadda zaki zama mai hadaka, zaki zama shugaba mafi inganci.
Kalmomi baza su raunata ki ba. Banda girman kai ko kuwa ki yi wa mutane mugunta. koda kin girme su. Koda kuna jayayya ne, kada ki sake ki zage su ko kuwa ki saka su jin kamar yara. Shugabanni masu gagarumi na bi da mutane da kyau.
Kina da yar uwa ko dan uwa da kika fi so? Dan Allah kice a’a. Nuna banbanci zai iya hana ki yin abun daya dace. Kuma idan kina son ki zama cikakkiyar shugaba, kada ki bi da kowane ma’aikatan ki fiye da sauran. Kada ki taba yin son kai. Muradin ki shine ki tabbata kowa ya ji dadin zuwa aiki kowane rana.
Dan uwan ki na bukatan taimako da aikin makaranta sa? Ki gaya masa kina goyon bayan sa. Abokiyar ki ta siyo wannan rigar a karshe bayan ajiyar da tayi na watani? Ki gaya mata cewa kina alfahari ta ita. Idan kika koya karfafa mutane yanzu, zai zo miki da sauki a lokacin da kika zama babban shugaba.
Share your feedback