Yadda zaku cika burin ku a shekarar 2018

Dabaru akan yadda zaku ci nasara

Dukkan mu nada buri da muke so mu cika.

Wa wasun mu burin mu na wani karamar lokaci ne. Misali kamar ajiyar kudi domin siyan wata riga ko waya.

Wa wasun mu kuma na wani dogon lokaci ne. Misali kamar koyar wani kwarewa, ko zama injiniya, ko mai zane, ko kuwa marubuce.

Koda menene burin, zaku iya cimma. Abun da muke bukatan yi shine yin imani da shi kuma da yin aiki domin muci nasara.

Kuna da wani buri da kuke son ku cimma? Ga wasu dabaru akan yadda zaku cimma…..

  • Kuyi setin wani buri na musamman – Kuyi tunanin abun da kuke son ku cimma. Kuyi setin burin. Ga misali, Ku karanta takardu hamsin a shekara, kuyi ajiyar siyan wani takalmi a watani takwas, da sauran su. Ku manna shi a wani waje da zaku riga gani.
  • Kuyi setin matakin da kuke bukatan daukawa domin ku cimma burin ku. Ga misali, Idan burin ku yin karatun wani takarda ne a mako, kuna bukatan yin rijista da wani dakin karatu ko kuwa idan kuna son kuyi ajiyar Naira dari biyu kowane mako, mai yiwuwa kuna bukatan fara wani sana’a domin ku samu karin kudi.
  • Ku nema ko ku karanta duk abun da zaku iya akan mutanen da suka ci nasara a abubuwan da kuke so. Ku tambaye su yadda suka cimma burin su. Ku koya daga masaniyar su.
  • Ku nema wani shirin horaswa ko kuwa wani kungiyar yan mata da zai taimake ku koya akan burin ku. Misali, zaku iya shigar wani al’ummar asusu domin ku koya yadda zaku yi ajiya. Wadannan kwarewar zasu taimake ku a rayuwa. Zaku iya samun sabobin abokai kuma ku hadu da tsaran ku dake da buri kamar ku. Wannan zai iya karfafa gwiwar ku.
  • Ku ajiye bayanan matsayin da kuka kai. Ku manna matakan da zaku dauka a wani waje da zaku iya gani domin kuyi makin su idan kuka cimma su. Wannan zai taimake ku lura da matsayin da kuka kai.
  • Kuyi imani da burin kuma kuyi kwazo. Ku amince cewa wasu lokuta zasu yi wuya. Amma ku san cewa zaku iya cimma babban abubuwa a rayuwa!

Kun shirya yin aiki domin cimma burin ku? Me kuke ganin zai iya hana ku cika su? Kuyi mana magana akan sa a wajan sharhi.

Share your feedback