Sai anjima, 2017!
Lokaci na tafiya. Minti daya ana watar Janairu, yanzu har an kai watar Disamba. Wasun mu sunyi abubuwa da yawa a wannan shekarar. Wasun mu kuma, ba sosai ba. Koda menene, abu mafi muhimmanci shine mun tsaya da karfin mu kuma bamu fid da rai ba.
Bari mu duba baya mu ga dukka abubuwan da kuka yi a wannan shekarar, ko? Kawai wani wasan nishadi ne da zai taimake ku setin shekarar 2018. Kun shirya? Muje zuwa:
Mataki na daya
Kunyi setin muradi a wannan shekarar? Mai yiwuwa kun so ku koya wani kwarewa. Ko kuwa kuyi ajiyar siyan wani karamin waya. Idan baku yi ba ko, kada ku dame kanku. Mafi karanci dai kuna da wani muradi. A shekara na gaba, zaku iya cigaba da ajiyar har sai kun cimma burin ku. Kada ku fid da rai.
Mataki na biyu
A maimakon tunanin abun da baku yi ba, ku maida hankali akan abubuwan da kuka yi. Kun taimake masu neman taimako? Kun daina wani hali mara kyau? Kun ci nasara a wani jarabawa? Ku kula da dukka wadannan abubuwan. Sune babban abubuwan da kuka cimma buri. Kuyi alfahari da kanku.
Mataki na uku
Ku rubuta kowane lokaci daya saka ku murmushi. Mai yiwuwa kun kara shakuwa da mahaifiyarku. Ko Kun samu wani labari mai kyau da kuke da saka rai akai. Tun da dai ya saka ku farin ciki, ya kamata kuyi shagali.
Mataki na hudu
Mun san cewa kun koya sabobin abubuwa. Yadda zaku yi magana. Yadda zaku samu sabobin abokai. Yadda zaku koya amfani da kwamfuta. Jerin abubuwan nada yawa. Duk sabon abinda kuka koya, tabbas ya taimake rayuwar ku. Shi ya saka ku zama mutane mafi inganci. Saboda haka, kuyi wa kanku tafi. Jeki yan mata!
Mataki na biyar
Ku tuna, kuyi godiya. Ku rubuta wasikar godiya wa mutanen da suka goya muku baya a wannan shekarar. Ku nuna gamsuwarka da dukkar zuciyar ku. Kuna bukatar mutane masu hali mai kyau a kusa da ku.
Toh gasu nan dai! Kunyi nishadi ko? Muna fatar munyi muku wahayi ku kara cimma wani buri a shekara na gaba. Muna nan, muna yaban ku a kowane mataki na hanya.
Me kuka yi a wannan shekarar? Menene kuka tsara zaku yi a shekarar 2018? Ku rarraba da mu a wajan sharhi.
Share your feedback