Ina son yin rubutu

Irene ta rarraba muradin ta na gaba dayan rayuwar ta

Ina kaunar yin rubutu. Koda yaushe ina yin tunanin fadin labarai masu ban mamaki. Amma ban san wata marubuciya ba. Ban tsammanin zai iya yiwuwa ba. Har sai da wata mata na musamman tazo makarantar mu.

A ranar, muna ta murnar zuwan ta. Ta gaya mana cewa ita marubuciya ce. Tun da take yarinya ta fara rubutu. Zuciya na ya fara bugu. Tana nan kamar ni!

Matar tace mutane sunyi mata dariya. Suka gaya mata cewa baza taci nasara ba. Amma ta tabbatar musu cewa sunyi karya.

Ya tayi? Ta karanta dukkan abun da zata iya nemo. Ta samu dabarun yin rubuta da kyau a shafin yanar gizo gizo. Na gaba, ta hade da wani kungiyar yin rubuta da wasu marubuta. Suna karanta aikin juna kuma suna bawa juna shawara masu taimako. Ta koya abubuwa sosai daga wajan su.

Matan tace akwai lokuta da taso da fid da rai. Amma babban abokiyarta ta bata shawara kada ta fid da rai. Babban abokiyar ta ta karfafa gwiwar ta.

Bayan lokaci kadan, ta fara tura labaran a wani mujalla. A farko, mujallar suka ki karben su. Sai bayan lokaci kadan, suka fara karban su. Suka biya ta ta kara rubuta labaran. Suka gayyace ta ta bada jawabi a wajaje masu kyau. Ma’abotan ta a dukkan fadin duniya suka yi mata rubutu cewa suna kaunar aikin ta.

Ta karfafa gwiwar mu muyi imani da kanmu, mu bi muradin mu. Ta gaya mana ta kusa ta wallafa takardar ta na uku. Kuma da taji abun da mutane ke fadi, da bata kai inda take yanzu ba.

Yanzu na kara yin kudurta zaman marubuciya. Idan zata iya yi, nima zan iya yi. Tana da ban sha’awa. Na fara yin dukkan abubuwan da tayi. Har nayi setin wani burin yin rubutu kowane rana. Kuma ina kan yi a kai a kai. Ina shirya yin aiki sosai domin na cimma burina. Na san cewa wata rana zan ci nasara.

Duk abunda kuke son ku zama, koda mai wasan ninkaya, ko mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin, ko kuwa marubuciya kamar Irene, zaku iya yi! Kada ku bari wani ya sanyaya gwiwar ku. Kada ku daina bin wannan muradin naku.

Menene burin ku? Zamu so muji daga wajan ku.

Share your feedback