Bai yi sauri ki fara ajiye kudi ba

Ke ma zaki iya fara ajiye kudi da sauri

Sau daya na karanta wani takada da wata yarinya mai shekaru goma sha uku ta rubuta. Akan yadda ta fara ajiye kudi a shekaru takwas. Abun ya bani mamaki sosai.


Ya akayi karamar yarinyar nan ta san abubuwa sosai akan samun karin kudi? Ni, ina kan tambayar iyaye na su bani N50 na siyo biskit! Bayan dana gama karanta littafin, naje na dubu asusu na( wajan ajiye kudi na) naga cewa ba komai ciki. “ina son na zama kamar yarinyar a,” na gaya wa kai na. Shekaru na goma sha biyar. Idan yarinya mai shekaru goma sha uku zata iya yi, toh bani da wani azuri kuma.

Shiyasa na gaya wa kai na, zan yi kokari na samu karin kudi na. Na fara ajiya daga kudin da nake samuwa daga wanke motocin makwafta na, da tsaftace gidan su ko kuma wanke kanyan su. Bayan wata biyu dana yi ajiya, na cire daga kudin na siya kayan kwaliyan fuska. “Ya zan taimake hana kai na cire kudi kuma?” na tambaye kai na. Zaki iya tsammanin abun da nayi?

Na gaya wa mahaifiya ta ina son na bude asusun ajiya na banki a waya. Ta bude mun da wayan ta. Bayan da ta kafa mun asusun wayan, muka je wajan Aunty Ayo, wata wakilin asusun ajiya na banki ta waya a ungwan mu, tana da kantin siyar da magani. Na bata kudi na sai ta taimake ni saka shi a asusun bankin. Da zaran da muka bata kudin ta taimake ni turawa a asusun banki na wayan, mahaifiyata ta samu jijjigar sako a wayan ta. Kudin na asusu na na banki! Tun Sannan ina ajiye kudi na ta hanyar nan. Kuma kudin na kara yin girma har a yau.

Ki hade da ni mu kara kudin mu tare, tambaye mahaifiyar ki ko wani abokin iyalin ki su kai ki banki. Ki shirya cika kakadda da kuma bada takardun ki domin ki bude wannan asusun bankin.

Zaki iya yin wa wani wakilin bankin waya a ungwan ku ko a kowane banki kamar, GTB, First Bank ko Skye Bank su taimake bude asusun banki na waya. Iyayen ki ko wani babba da kika yarda da zasu iya taimakon ki yanke shawara akan asusun banki na waya ko banki mara matsala da zaki iya budewa.

Share your feedback