Ki sa ya zama abokin ki kawai, ba tare da matsala ba.

Koda baki son shi, zaku iya abokantaka

Tunanin ku (4)

Zan iya abokantaka da namiji? Amsa wannan tambayen zai yi wahala. Gaskiyar shine idan kika fara balaga canji na zuwa a jikin ki, da tunanin ki da kuma zumuncin ki da samarai.

Wannan zai iya zama kauna da kike wa wani yaro na musamman ko canji a abokantakan ki da samarai da kika girma da ko kuwa wani da kike jin dadin magana da ko kwashe lokaci da.
Idan kina kwashe lokaci sosai dasu wadannan sinadarin kimiyya na jikin ki zasu iya rikitar da ke. Idan kuna sha’awar juna mai sauki ne ya bunkasa zuwa wani abi. Amma idan baki son wani abun soyayya da shi kuma shi yana so fa? Abubuwa zasu iya janyo matsala.

Ga wasu hanyoyi da zaki gina abokantaka da samarai kuma ya tsaya a hakan.

Ki Kafa iyaka
Ki fahimtar dasu cewa kina son ku zama abokai ne kawai. ki kafa makura. Ga misali, babu rungumen juna, babu tabi ko magana a waya a cikin dare. ki yanke shawaran abun da zaki iya yi sai ki manne da shi. ki tabata cewa ya fahimta cewa abokantakan ku ba zai canza zuwa wani abu ba.

Ku fita a kungiya
Ki kunsa sauran abokan ki a yawon ku. Ki tabata kowa ya biya kudin sa. Wannan zai nuna cewa shi daya daga cikin kungiyar abokan ki ne.

Ki zama abokiyar arziki ( ki tabata cewa shima abokin arziki ne)
ku goyo bayan juna. Ku ringa fadin wa juna gaskiya. Ki saurare shi sai ki kokari ki taimaka masa da matsalolin shi a lokacin da zaki iya. Ki dauka sha’awa a abubuwan da yake so. Kada ki tsamnanin zai rika yin miki alfarma. ki tabata shima yayi miki kamar haka.

Kada ki boye abokantakan ku
Mai yiwuwa mutane baza su fahimta abokantakan ki da namiji kamar ba komai tsakanin ku ba. Saboda haka, zaki ji kamar ki aje si sirri. kada kiyi haka. Ki gaya wa iyalai ki akan shi, ki gabatar dashi a wajan sauran kawayen ki, idan baki boye abokantakan ku ba zai nuna wa mutane da kuma shi cewa babu komai tsakanin ku kuma zai tabatar cewa babu komai da zai faru.

Kin san wani yaron dake yawan damun ki kuma bai son yaji a’a, ko akwai wani yaro dake baki tsoro kowane lokaci da yake kusa da ke. Muna baki shawara ki dai na ganin yaron nan. ki kai karan shi a wajan wani babba nan take.

kina da wani abokin arziki namiji? Gaya mana masaniyan ki a shafin sharhin mu.

Share your feedback

Tunanin ku

Saboda tana son shi

March 20, 2022, 8:04 p.m.

my boyfriend love me and we can help ourselves with sex

March 20, 2022, 8:02 p.m.

ni babbane ba yaro bane fa

March 20, 2022, 8 p.m.

Latest Reply

munga kuturu