Karin siddabaru akan yadda zaki kauda hatsar
Duk mun ji irin wannan kawazuci. Wanda kike ji idan kina tafiya ke daya a kan layi. Baya dadewa kafan karan su fara zuwa- kukan mage, ko na fito, ko wani magana marasa kyau. Wasu lokuta kina tafiya da sauri ko ki kama gudu. Wasu lokuta ma, kina koma gida.
Kamar yan mata, muna fuskance abubuwa masu bada tsoro kusan kowane rane. Wa dukkan mu, yana da muhimmanci mu tsirata kan mu kuma muyi farin ciki. Siddabarun nan na nan kasa zasu taimaka. Bari mu fara.
Kada ki tsaya a makarkataa ke daya
A wajan jama’a, ki guje tsayawa a boyayyen makarkataa ke daya. Ki tsaya a wajan da akwai mutane. Ki zauna a wajan da akwai isashshen haske da kuma mutane.
Shakatawa a kungiya
Duk sanda kika fita, Yana da kyau ki tsaya da kungiyar abokai da kika yarda da. Akwai Tsira a irin kungiyar da kike bi.
Kada ki bar gida idan baki gaya wa wani inda zaki je
Kafan ki bar gida, ki tabata cewa wani ya san inda zaki je. Ki bar adireshin ko lambar wayan idan zaki iya.
Ki koya cewa a’a
Kada kiji tsoro kice a’a akan gabatowar da baki so. Idan wani nason kiyi abun da babu gamasashshenbawa, kice a’a kawai.
Babu sirri: Kai rahoton kowane halayyar zargi daga wajan yan maza
Ki yarda da ilhaman ki. Idan kina ji kamar baki jin daidai da wani mutum ko wani hali, mai yiwuwa kina da gaskiya. Kada ki rike abun dake tsorata ki a zuciyar ki. Ki gaya wa wani babba da zai iya taimakon ki.
Ki tuna ki raba wannan da wasu abokan ki. Idan yazo lokacin tsirata kanki, duk muna nan tare. kina da wani siddabarun tsira? gaya mana a shafin sharhin mu a nan kasa.
Share your feedback