ki tsaya wa abun da kika cancanta
Yara mata nada hakkoki. kamr kowane mutum a al’ummar mu. Abun muhimmanci ne mu san menene wadannan hakkokin.
Saboda mu san abun da yake da kyau da kuma wanda keda kuskure.
Saboda mu san lokacin da zamu iya magana da kuma kai rahoto.
Bamu kankani mu san hakkokin mu ba.
Kin san hakkokin ki na asali?
Ga wasu abubuwa da kowane ‘yar mace ya kamata ta sani:
kina da hakkokin samun ilmi
kowane yaro nada hakkokin samun ilmi. A yayin da samun ilmi na kwarai hakkokin ne, ba lalai bane ilmin ki ya zama na ajin karatu kawai. Zai iya zama a wani kwarewa ko kasuwanci da kike koyo.
Idan muka samu ilmi ko muka samu aka horas damu a wani kasuwanci muna da tabbaci na rayuwa na nan gaba mai inganci.
kina da daman yin iko da abun da zai faru da jikin ki
jikin ki mallakin ne. ya kamata a dauke shi tamkar da mutunci.
Ba wanda keda daman cin zarafin ki ta jima’i ko ta duka.
Kada mu sake muji tsoron yin magana idan wani ya raina jikin mu.
Kina da hakkin cewa a’a wa aure da wuri
kina da hakkin yanke shawaran lokacin da kuma wanda za ki aure. An matsa miki lambar kiyi aure? kiyi wa iyayen ki magana ko wani babba da kika yarda da. Kiyi musu magana da mutunci akan abun da kike so. Ki bayana musu akan dalilin da yasa baki son kiyi aure yanzu. ki samu wani ko wata babba da kika yarda da kiyi musu magana akan wannan. zai iya zama malamar ki na makaranta ko wata yar dangin ku.
Na tilas ne mu koya yin magana wa kanmu.
Gaya mana akan halin da kika samu kanki da kika yi magana? ya kika yi shi?
Share your feedback