Kudi baya siyan kauna

Kauna na bai da farashi – Jennifer Lopez

Nawa ne darajar kauna? Idan aka ce ku sanya farashin kaunar ku, nawa ne zaku saka?

Na tabbata kuna kan tunanin farashin. Kun san meyasa?

Saboda kauna bata da farashi.

Kowa na son kuana.

Yawancin yan mata na son kauna kamar na wasu gimbiyoyin nan daga labaran yaranta.

Wasu mutane zasu iya yin komai domin su samu kauna ko kuwa su bada kauna.

Mai yiwuwa kun taba ji akan wasu yan mata dake musayar kaunar su da wayoyi, ko kayan ado, ko kuwa kudi.

Ko kuwa yan maza dake yin haka ko dake kokarin samun hankalin yanmata da kyaututtuka.

Amma mun san cewa kauna ba abun da zamu iya siyar ko siya bane.

Kada ku bari wani ya kokari ya ci hancin ku domin ku so su.

Kyaututtuka daga wani dake kaunar ku nada kyau. Amma kaunar na zuwa kafar kyautar. Bada zagaye ba.

Idan mutane na kaunar juna, zasu iya musayar kyaututtuka domin su nuna kauna. Amma idan wani ya baku kyuata domin ya saka ku son su ko kuwa ya saka ku yin wasu irin abubuwa, toh akwai matsala.

Akwai wani saurayi a ungwan ku dake yawan muku tayin kayan zaki, ko kudi, ko kuwa katin waya domin kaunar ku?

Akwai wani dake yawan gaya muku kuyi soyayya dasu dan kawai suna da kudi?

Yau, muace “A’a”

Idan basu barku ba, ku kai rahoton su a wajan wani amintaccen mutum da kuka yarda da ko kuwa iyayen ku.

Mu Springsters ne.

Yar Springster mace ce mai cin gashin kai.

Kaunar ta bashi da farashi. Tana kauna da daraja kanta domin kanta ba akan abun da take da shi ba.

Baza a iya siyan ta ba. Ta san hanyoyi masu tsira da zata samu kudin kanta

Ta san abun da take so kuma tana bin sa. Tana da karfi kuma ta sani. Tana nan kamar Funmi. Ku latsa a nan domin ku karanta kan Funmi.

Wani namiji na muku tayin kudi? Ya kuke bi dashi? Kuyi mana magana a nan wajan sharhi.

Share your feedback