Sabuwar dabarar ajiya ta

Chinelo ta gaya mana dukka

A farkon shekarar nayi alkawarin fara yin ajiya. Amma dai zai dan yi wuya ne. Akwai abubuwa da yawa da za’a iya yi, ko a gani, ko kuwa a siya. Da dukka wadannan abubuwan dake daukan hankali, yin ajiya bai iya mun aiki ba.

Amma bazan fida da rai ba. A gaskiya, kwanan nan nayi magana da Inna na. Ta iya yin ajiya da dabara, shiyasa na tambaye ta shawarar abun yi. Ta gaya mun cewa kowa zai iya koyan yin ajiyar kudi– tunda dai suna kokarin gwadawa. Sai ta ban dabaru guda uku masu sauki da zasu taimake ni yin ajiya da kyau. Yanzu na shirya kara gwadawa.

Na farko, ina son na rarraba dukka abubuwan dana koya da ku. Abun da abokai ke yi wa juna kenan ko? Ga sabobin dabarun ajiya na:

Sauki yafi
Zan fara da yin setin wani manufa. Ba wani babba ba, amma wani karami da zai yi muku saukin cimma. Wannan yana nufin cewa zan ajiyar siyan kananan abubuwa kamar ‘yan kunne, kayan dadi da nake so da kuma kudin mota. Inna na tace idan na cimma muradi na, zai karfafa ni nayi kokarin cimma wani babban buri kamar wani atamfa mai kyau, zan iya yin komai idan na saka rai– Kuma zaku iya.

Ku kula da matsayin da kuka kai
A karshen mako, zan lissafa nawa nayi ajiya. Wannan zai taimake ni dago kuskure na tun da wuri, sai na gyara su. Kuma zai karfafa ni na cigaba. Gaskiyar shine, ba akan yin ajiya bane kawai. Akan yin ajiya da wayo da kuma cimma buri na. Bada jimawa ba zan saba da yin ajiya da har zan kware.

Yin shagali a karshe
Dole na hana kai na abu daya ko biyu domin na cimma buri na. Ga misali, dole na daina siyan kayan kwadayi kowane rana domin nayi ajiya a maimako. Eh, zai yi wuya, amma na san cewa zanyi nasara a karshe. Shiyasa da zaran na cimma burina zanyi shirin yin shagali da siyo wa kaina kwallin kayan kwadayin da nake so.

Kuma Inna na zata yi alfahari dani.

Toh shikenan, Springsters.

Ku tuna, muna tare a cikin wannan. Zamu iya yin sa!

Kuna da wasu dabarun yin ajiya?

Ku ajiye mana a nan kasa.

Share your feedback