Iyaye na basu goyon bayan muradi na

Kuyi imani da kanku koda menene

Kowa na fadin cewa kuna da murya mai dadi. Ko kuwa kun iya ilmin lissafai sosai. Ko kuwa kuna iya cusa wa kowane mutum ra’ayi ya siyo kowane abu.

Wadannan kalmomin na nufin abubuwa da yawa muku. Saboda muradin ku na zama mawaka. Ko kuwa na komawa makaranta. Ko na fara wani sana’a. A takaice dai, kun kosa ku cimma muradin ku. Amma akwai matsala daya: Iyayen ku basu amince ba.

Mai yiwuwa suna son ku tsaya a gida. Mai yiwuwa suna tunanin cewa bai kammata yan mata su samu nasu kudi ba. Kunyi kokari ku canza musu ra’ayi. Kun zauna so dayawa ku tattauna dasu. Amma babu abun daya canza.

Ba komai bane idan kuka yi bakin ciki da wannan al’amarin. Amma ku tuna, an haife iyayen ku kafan ku. A lokacin su, yan mata basu saba da samun wasu abubuwa ba. Mai yiwuwa ma baza su gane abun da kuke so ba. Kuyi hakuri dasu. Kada kuyi fushi ko tagumi. Zaku kara bata abubuwa ne.

Baza ku iya tilasta mutane suga abun da kuke gani ba. Bazu ku iya yin iko da yadda suke ji ba. Abun da zaku iya yi shine ku kara aiki da kyau. Ku kara tura kanku kuma kuyi iya kokarin ku.

Yin imani da kanku idan iyayen ku basu yi ba ba abu mai sauki bane. Amma zai iya faruwa.

Na farko, Ku nemo sauran mutane dake goyon bayan muradin ku. Zai iya zama yan uwan ku, ko Inaan ku, ko babban abokan ku, ko kuwa wani amintaccen babban mutum. Idan abubuwa suka yi tauri, zasu karfafa gwiwar ku. Mai yiwuwa ma su taimake ku yin wa iyayen ku magana. Kuma mai yiwuwa yayi aiki.

Na gaba, ku samu wasu mutane da suka ci nasara da irin muradin ku. Ku cinka wani daga ungwan ku ko kuwa wani ungwa dake kusa da ku. Ku bincika yadda suka cimma burin su, sai ku gaya wa iyayen ku akan sa. Wannan zai taimaka ya cusa wa iyayen ku ra’ayi cewa kuma zaku iya cin nasara.

Na karshe amma ba kalla ba, kada ku fid da rai. Idan kuna son kuci nasara, ya kamata ku kudurta. Saboda haka, ku shiga wannan gasar wakan. Ku cigaba da yin lissafi. Ku koya wani sabon kwarewa. Wadannan abubuwan zasu kai ku sama.

Bayan lokaci kadan, iyayen ku zasu fara jin ku. Zasu yi alfahari daku. Zasu gaya wa dukka duniya ku yaran su ne. Baku yarda ba ko? Ku tsaya ku gani.

Menene babban muradin ku? Ya iyayen ku suka ji akan sa? Rarraba labaran ku.

Share your feedback