Iyayena na son zama cikakkiya….

Amma ni kawai in son nayi abun da nake so!

Iyayena na yawan takura mun akan wani abu. Kamar, yadda nake son saka riga da wando dake saka ni walwala. Mahaifiyata tace ya kamata na riga saka dogon fatari da kuma riguna. Kuma tace ina yawan kwashe lokaci a kan waya. Ina ji kamar ba zan iya yin nishadi kuma ba.

Mahaifina ma na takura mun. Ina son yin aiki akan kwamfuta. Ya tsane ra’ayina na yin aiki da kwamfuta. Ya saka ni cire darasin daga jarabawar JAMB.

Dan uwana na iya yin duk abun da yake so. Abun na bata mun rai sosai.

Kwanan nan mahaifiyata ta fara suka abokai na. Tana ganin basu da isasshen wayo.

Ina da abokai mata da maza, kuma ina kaunar su. Koda yaushe suna goyon bayan burina da muradi na. Mahaifiyata tana ganin zasu janye mun hankali kuma mahaifina yace bai kamata mace me shekaru na tayi abokantaka da samari ba. Yace mutane zasu fara zato. Ina ganin abun yayi yawa. Abokai na na mun dariyar yadda iyaye na ke tsananta mun rayuwa.

Za’a yi bikin ranar haihuwar abokiyata Anita a karshen mako, kuma iyaye na sun ce ba zan je ba. Suka ki gaya mun dalilin.

Ina girmama iyaye na. Na san cewa suna kokarin kare ni ne, amma kuma ina son na samu ikon yanke shawara game da abubuwa da suka shafe ni. Ina ganin na nuna musu cewa zasu iya yarda dani, saboda haka ina fatan zasu yarda mu zauna mu tattauna wannan.

Na dauke ni lokaci kadan na kwantar da hanalki na nayi musu magana ba tare da fushi ba. Dana shirya, na gaya musu da hankali cewa ina alfaharin macen da nake zama. Na gaya musu cewa ina karatu sosai kuma ina daraja abokai na - Kuma ina son su bani goyon gaya

Na dan basu lokaci su fadi damuwan su, kuma suka girmama ra’ayi na. Bayan da muka gama magana, iyaye na suka fara sha’awar yadda nayi girma. Suka amince cewa zasu kara goya bayan duk shawarar dana dauka. Mahaifiyata ma tayi alkawari cewa zata daina saka ni saka dogon riguna.

Kuna ji kamar iyayen ku ko kuwa masu tsaran lafiyar ku na tsananta ku? Kuyi wa babban yaya magana akan yadda kuke ji a sashin sharhi.

Share your feedback