Sabuwar shekara sabon ni

Dabarun kara inganta lafiyar ku

Barka da sabon shekara Springers!

Sabon shekara na zuwa da daman tsara sabobin abubuwa da zaku yi da kuma setin sabobin buri.


Ku samu sabobin abokai. Ku karanta takardu. Ku koya wani sana’a ko kuwa wani kwarewa. Kuyi magana da samarin da kuke so. Kuyi ajiyar kudi. Wadannan ne wasu daga cikin abubuwar da zaku iya yi.

Wannan shekarar, zaku iya kara samun lafiya da farin ciki. Ga wasu dabaru masu sauki da zai taimake ku yin wadannan!

Kuci lafiyayar abinci

Kuna bukatan sinadaran kara lafiya sosai domin girman jikin ku. Kuyi wa jikin ku alfarma kuci lafiyayar abinci. Ku samu yalwar sinadaran gina jiki kamar wake, kwai, kifi ko kuwa nama.
Kuna son shan kayan zaki? Kuyi seti wani buri akan yadda zaku rage shan kayan zakin nan. Ga misali, zaku iya yanke shawarar shan kayan zaki guda daya a mako. Misali, zaku iya setin burin shan kofin ruwa kowane safe nan da nan da kuka tashi. Kuyi setin burin cin ‘ya’yan itatuwa da kuma ganye koda yaushe.

Ku motsa jiki
Motsa jiki na taimakon lafiyar jikin ku. Zai kara karfafa zuciyar ku kuma ya kara muku farin ciki. Bai da wuya. Zaku iya yin gudu da hankali. Ko kuyi tafiya da wata abokiyar ku. harda yin ruwa wa wakan nan da kuke so.

Ku gwada yin wani sabon abu
< Ku kasance masu sha’awa akan abubuwa dake kusa daku. Duk lokacin da muka gwada yin wani sabon abu, muna koyo ne. Yana taimakon mutane kara girma. Ku gwada wani sabon abinci. Ku karanta wani irin takarda daban. Ku koya yadda ake yin wani wasa ko kuwa wasannin motsa jiki.

Ku gina kanku
Halin mutum komai ne. Dole kuyi imani da kanku. Ku tunatar da kanku yadda kuke da gagarumi. Kowane safe, ku kali madubi kuce Ina da kaifi, ina da karfi, ina da kyau, zan iya yin babban abubuwa, babu kamar iri na.

Yan Springster shekarar ku zai iya kasance mai kyau. Kuyi aiki sosai domin ya auku. Ku zama matsaya. Kuyi imani cewa zaku iya.

Akwai wani sabon abu da kuke son ku gwada yi a wannan shekarar? Kuyi mana magana akan sa a wajan sharhi.

Share your feedback