Baku kankanta ku cimma muradin ku ba!

Ku sadu da wannan yarinya mai shekaru goma sha bakwai dake rubuta tsarin dokokin kwamfuta

A ranar ta goma sha daya a watar Oktoba, gaba dayar duniya na yin shagalin Ranar ‘Yar Mace. Domin muyi shagalin sa, muna son mu raba labarin wata yarinya mai shekaru goma sha bakwai dake yin abun ban mamaki.

An taba gaya muku cewa baza ku iya cimma wani abu saboda ku mata ne ko kuwa domin wajan da kuka fito daga?

Kada ku maida hankali ga wadannan mutanen - Zaku iya zama duk abun da kuke so. Kamar Sharon Okpoe, mai shekaru goma sha bakwai da ta zama mai rubuta tsarin dokokin kwamfuta kuma ta mai da shi sana’ar ta.

Sharon ta fito daga wani al’umma a jihar Lagos dake kasuwancin kama kifi, kuma ita ce ‘yar na goma sha daya a wajan mahaifin ta masunci da kuma mai kasuwanci, ta zama mai farin jini a yanar gizo gizo bayan da ta kirkira wani shafin yanar gizo.

Amma nasarar ta bai faru a cikin dare ba. Ya dauke horaswa da yin aiki sosai. Duk da cewa iyayen ta basu je makaranta ba, muradin ta shine ta karanta darasin injiniyar manhajar na’urar kwamfuta a jami’ar Harvard.

Saboda haka, da Kungiyar rubuta tsarin dokokin kwamfuta na yan mata, wani kamfani da Abisoye Ajayi-Akinfolarin na Pearl Africa Foundation ta kirkira suka yanke shawara su koyar da yan mata a al’ummar ta yadda ake rubuta tsarin dokokin kwamfuta, Sharon tayi sauri ta dauki wannan damar. Wannan shirin ne hanyar kara inganta rayuwar ta da kuma cimma burin ta.

Ta shirin, Sharon ta koya yadda ake rubuta tsarin dokokin kwamfuta da kuma kirkira shafukan yanar gizo da kuma aikace-aikacen tafi da gidanka.

A lokacin horar ne ta kirkira wani shafin yanar gizo domin ta taimake iyalin ta da sauran yan al’ummar ta samun kudin kwarai.

Sharon ta lura cewa ba’a biyan masunta kudi sosai, ba kamar yan kasuwa dake siyar da kifayen ba.

Da taimakon sauran yan mata, ta kirkira wani shafin yanar gizo da ake kira Makoko Fresh. Ta kirkira shafin yanar gizon domin ta taimake hada kasuwancin masunta da abokan kasuwanci masu son kifi.

Yau Sharon ta zama karamar shugaba. Manyar gidan kofofin watsa labari kamar BBC Africa da kuma CNN na yin mata zantawa

Ya dauki imani da kanta, da kuma bin muradin ta kafan wannan ya auku.

Zaku iya zama kamar Sharon.

Ya zaku yi? Toh gashi nan;

  • Kuyi imani da kanku
  • Ku samu muradi babba kuma ku yi aiki sosai domin ku cimma burin ku
  • Kada ku saurare mutane dake fadin muku cewa baza ku iya ba.
  • Ku shiga ayyuka a al’ummar ku ko kuwa a makarantar ku da zai iya taimakon ku koyan sabobin kwarewa.

Ku karanta karin abubuwa akan Sharon a nan

Menene babban muradin ku? Ku rarraba da mu a sashin sharhi.

Share your feedback