Kin shirya wa abun da zai biyo baya?
Kina sha’awar wani yaro? Samarai sun fara tashin ki? abokan ki na yawan maganan samaran su? kina ji kamar ke daya aka bari a baya mara saurayi?
A wannan shekarun ba komai kiji burin sanin akan maza. Amma ga wasu abubuwa da zaki tambaya kanki:
Zan iya bi da shaukin?
Daga waje, bamu ganin yanki mai wuya na soyayya.
Samun saurayi na zuwa da matsin lambar sosai.
Wasu lokuta masu soyayya na fada.
Yana zuwa da abubuwa da yawa da zai sa ki sa wani farin ciki.
Mu tabbata cewa mun shirya bi da dukka kawazuciya dake zuwa da soyayya.
Na shirya yin jima’i?
Ba lallai bane wai idan kina da saurayi wai sai kun yi jima’i.
Amma zai iya wuya kice a’a.
Zai iya matsa miki lambar. Mai yiwuwa ki so kiyi.
Amma yin jima’i na zuwa da kasada.
Akwai hatsarin kama cuta da kuma daukan ciki.
Ya kamata mu san ko mun shirya wa kowane sakamakon.
Na san kai na da kyau?
Me nake so? menene bana so? me nake so daga rayuwa?
Idan baki san kanki ba, rayuwa zai zama akan abun da saurayin yake so. Zaki koma yin abubuwan da kawai kisa shi farin ciki. Koda ma basu da kayu miki.
Ya kamata mu kara gane kan mu kafan mu fara.
Ina da Lokaci?
Yin samarai na daukan lokaci sosai. Yawancin mu nada makaranta ko aiki, ko aikace aikacen gida da kuma alhakin iyalin mu.
Rarraba lokaci tsakanin samarai da rayuwa na asali ba abu mai sauki bane.
Ya kamata mu tabbata cewa zamu iya yin dukka abubuwan da ya kamata muyi.
A karshen, ke daya kika sani ko kin shirya yin saurayi.
Kada ki yarda abokan ki su matsa miki lambar kiyi abun da baki shirya yi ba. Kiyi tunanin abun da kike so. Kiyi tunanin wajan da kike son kije a rayuwa.
Kiyi tunanin asalin ma’anan fara soyayya. Ki fara idan kina ji kamar kin shirya.
Kin fara yin soyayya? Kina tunanin yin soyayya? kiyi mana magana a shafin sharhin mu.
Share your feedback
Tunanin ku
Nashirya
March 20, 2022, 7:53 p.m.