Yin aiki zuwa rayuwa na gaba mai inganci
Kwatanta kanki a shekaru uku daga yanzu.
Me kika gani? Kinji dadi da abun da kika gani?
Gaskiya ne cewa ba wani daga cikin mu da zai iya ganin rayuwar mu na nan gaba. Amma abubuwan da muka yi yau su ne zasu gyara abun da zai faru gobe.
Domin ki kai rayuwar na nan gaba da kike so, yakamata ki zama a hanya na kwarai.
Wannan yana nufi cewa zaki dauki shawara na kwarai game da ilmin ki, da aikin ki, da kuma rayuwar ki gaba daya.
Ya zamu shiga kan hanya madaidaiciya?
Samu ilmi
Zai iya zama zuwa makaranta ko koyan wani sana’a. Idan kika kara ilmi da kwarewa, zaki fi samun kaddara a rayuwa.
Kada wani abu ya dauke hankalin ki
Abokai nada muhimmanci. Haka ma samarai. Amma abun da yafi muhimmanci shine rayuwar ki na gaba. Kada ki yarda wani ya fidda hankalin ki a muradin ki
Ki nema abun nan da kike matsanancin so
Menene abun nan da kika iya yi sosai? Menene abun nan da kike son yi? Da zaran kika sani, kiyi kokari ki bunkasa wannan kwarewar. Baki san iyakan da zai kai ki ba.
Ki tsara abun da zaki yi
Menene muradin ki? Menene kike bukata ki kai wajan nan? Akwai wani horo na musamman da kike bukata? Kudi nawa kike bukata? Ki rubuta shi sai ki tsara yadda zaki dauki kowane mataki.
Ki gina wani kwararrun abokantaka da zai goya miki baya
Ki kewaye kanki da abokai da suka imani da ke da kuma zasu karfafa gwiwan ki. Ki nema mutane da kike martaba da kuma kin yarda zasu baki shawara.
Kina ganin kina hanya na kwarai? Kiyi magana da wani mahaifin ki ko wani babba da kika yarda da akan muradin ki. Zasu iya taimakon ki fara yanke shawara na kwarai.
Gaya mana abun da kike yi domin ki tsaya a hanya na kwarai.
Share your feedback