Siddabaru guda shida da zai taimake ki iya magana a gaban mutane
Zaki yi magana a gaban wasu kungiyar mutane ko kuwa a majalisan makarantar ku.
kin riga kin haddace dukkan rubucen ki. Kin san abun da zaki ce. Kina nan a shirye.
Kin hawa dakalin. Kowa na kallon sai…..kalmomin suka ki fitowa.
Menene ma ya kamata kiyi magana akai? Meyasa kin kasa tuna komai?
Tsoro, tsoro, tsoro!
Akwai mutane kadan dake walwala suyi magana a cikin kungiyar mutane da yawa.
Wa yawanci, kwarewa ne da zaki koya.
Kina tsoron magana a cikin jama’a? Ga siddabaru guda shida da zai taimake ki cire kuskuren magana a cikin kungiyar mutane da yawa.
Kiyi kokarin saka kaya me kyau. Ki saka rigar da zaki iya walwala a ciki. Ki saka rigar daya dace da lokacin. Babban sirri: ba akan su bane. Akan ki ne. Ki fara gina aminta ki da wuri zaki ki ji daidai a saman matakin.
Ki fara gwajin a gaban mutanen da kike walwala da. Kiyi gwajin a gaban madubi. Kamar yin wasa da kayan aiki ko kuwa wasan motsa jiki, magana a gaban mutane abu ne da zaki iya ingantuwa idan kika cigaba da yi.
Ki tunatar da kanki ki huta. Kiyi nunfashi ta hancin ki. Zai taimaka kula da bugun zuciyar ki kuma zai hana ki yin fargaba.
Ba da gunki ko mutmin na’ura kike bagana ba . Kina magana da mutane kamar ki ne. Ki karya katanga tsakanin ke da masu sauraro. Ki tambaye su ya su ke kuma kiyi musu magana kai tsaye.
Idan kika yi kuskuren furtar kalma ko kuwa kin manta da wani yanki a maganan ki, kada ki tsaya kice yi hakuri! Ki cigaba da tafiya. kiyi murmushi. Ki hada ido dasu. Aminta abun zuciya ne.
Baki son ki zama mai i’ina idan kina magana da kungiyar mutane. Kina magana akan wani darasi da baki sani sosai ba? Kiyi amfani da yan kankanin rubuce rubuce a takarda ki tunatar da kanki abubuwan da kika rubuta. Ki tuna kada ki ringa kallon su gaba kowane lokaci!
Allah ya bada sa’a yan mata! Kuma ku tuna: Duk mun taba samun kan mu a irin al’amarin nan!
Share your feedback