Ku baza kaunar Springster

Akwai farin ciki a cikin rabo

Menene abun da kuka fi so akan kasancewa yan Springster? Labaran ne, ko sharhunan ne, ko kuwa Babban Yaya ne? Koda menene, mun tabbata cewa Springster ya hadu! Shiyasa bai kamata mu bar abokan mu a baya ba.

Ya kamata mu yan Springster mu baza kauna. Kowa zai iya shiga. Kofofin mu a bude ne. Ga hanyoyin masu sauki da zamu iya gaya wa abokan mu:

Rarraba labaran mu
Idan wani labarin Springster ya koya mana darasi mai daraja ko kuwa ya tuna mana da wata abokiya ko wani hali da wata yar iyalin mu ke ciki, mu kokari mu rarraba da su. Zamu iya yin wannan ta shafin facebook, ko whatsapp ko kuwa muyi mata magana kawai. Kuma mai yiwuwa ya karfafa ta hade da mu.

Magana nada kyau
Idan muka koya abun muhimmanci a nan, kada mu ajiye wa kanmu kawai. Ga misali, idan yan uwan mu ko kuwa abokan mu suka lura cewa mun kara samun tabbaci da karfin yin magana, mu gaya musu akan Springster. A ta nan, suma zasu hade da mu kuma su koya abu daya ko biyu.

Koyarwa nada kyau
Ilmi yafi kyau idan aka rarraba. Saboda haka idan muka koya wani kwarewar hannu a nan (kamar yadda ake yin jakan atamfa), mu koya wa yan uwan mu ko abokan mu. Idan muka gano akan tsarin dokokin kwamfuta, mu gaya wa wannan abokiyar mai son aikin kwamfuta. Mai yiwuwa zata so ta san in da muka samo bayanan. Sai bayan lokaci kadan, ita ma zata zama yar Springster.

Ku tuna, mu yan Springster na nan tare koda yaushe, bamu zaman kadaici. Daya daga cikin sirrin mu kenan. Saboda haka, ku je ku baza kaunar Springster a nesa da kusa. Duniyar tayi girma ta isa dukkan mu.

Ta ya kuma zamu iya baza kaunar Springster? Ku gaya mana a nan kasa.

Share your feedback