Tsare kanku a yanar gizo gizo

Abun da kuke bukatan sani

Yanzu kuka fara amfani da yanar gizo gizo? Mai yiwuwa yanzu kuka samu wayar ku, ko kuwa kuka fara Facebook. Mai yiwuwa yanzu kuka fara amfani da whatsapp ko kuwa eskimi.

Kasancewa a kan layi wani sabon duniya ne dabam. Amma kamar asalin duniya, yana da bangeren sa mai kyau da kuma mara kyau.

A yanar gizo gizo zaku iya haduwa da sabobin abokai, zaku iya samun bayanai akan komai, kuma ku koya sabobin abubuwa.

Duk da haka akwai wasu hatsarori da zaku iya fuskanta a yanar gizo gizo. Shiyasa kuke bukatan tsare kanku a yanar gizo gizo.

Kasancewa da tsaro a yanar gizo gizo, na nufin cewa kuna sanne da hatsarorin yanar gizo gizo kuma kun san yadda zaku bi dasu. Wasu kasada da zaku iya fuskanta a yanar gizo gizo shine:

Tsangwamar Yanar gizo gizo
Kamar sharhuna ko sakonnin rubutu mara kyau, masu lahani ko na barazana. Mai yiwuwa mutane su fadi abubuwa mara kyau a yanar gizo gizo. A maimakon yin musu farmaki ku tura musu sakon rubutu kuce, “Zanyi godiya idan kuka daina rubuta abubuwa mara kyau a shafi na” Ko kuwa ku toshe su daga shafin ku. Idan kuna son ku toshe su, kuje shafin su. Ku danna wadannan bakakken digon guda uku dake kusa da wajan sakonni. Wasu jerin rubutu zasu fito, sai ku danne wanda yace “toshe”. Kuma zaku iya kai rahoton su a Facebook ko kuwa whatsapp.

Nuna wasu irin abubuwa kamar bidiyon batsa ko kuwa tashin hankali
A wasu shafukka zaku iya toshe ganin irin wadannan abubuwan, zaku iya zuwa wajan saitunan ku duba ko zaku ga wajan da ake toshe mutane. Ku duba ku ga ko zaku iya toshe ganin irin abubuwan nan. Idan aka saka irin wadannan abun ko aka tura muku, zaku iya daina bin su ko kuwa ku toshe su daga shafin ku saboda su daina tura muku sakonni, kuma baza ku cigaba da ganin abubuwan da suke sakawa ba.

Masu farauta a yanar gizo gizo
Ana nufin mutane masu amfani da yanar gizo gizo domin su kokarin bidan yara ko yan mata kamar ku saboda suyi musu lahani. Mai yiwuwa aniyar su su raunta ku ne ko kuwa su fara wani dangantaka da bai dace ba. Saka bayanan ku na sirri a yanar gizo gizo zai iya saka ku ko abokan ku da iyalan ku cikin matsala. Idan wani ya tura muku sako yana tambayen ku adireshin ku ko hotunan ku, kuyi watsi dasu ko kuwa ku toshe su daga shafin ku.

Kuyi hankali da duk wadanda kuke haduwa da a yanar gizo gizo, harda mutanen dake kama da masu hankali, domin zasu iya jawo muku lahani. ku toshe kowane mutum dake son ya saka ku yin wani abu da zai hana ku sakewa koda kun san su.

Muna son ku tsare kanku idan kuna amfani da yanar gizo gizo, koda ta wayar hannu ko kuwa a wajan da ake biyan kudi domin a yi amfani da yanar gizo gizo.

Kun samu abokai a yanar gizo gizo? Akwai wanda yaso ya hana ku sakewa a yanar gizo gizo? Ku rarraba masaniyar ku na yanar gizo gizo a sashin sharhin mu.

Share your feedback