Siddabaru guda uku akan fasaha da zai taimake ki ajiya
Saboda ajiya nada hazak’a
Fasaha ya canza abubuwa da yawa a nan. Yanzu yana da sauki wa mu yan mata mu cigaba da tuntuba juna. Amma akwai abubuwa fiye da haka da zamu iya yi da wayoyin mu. Kamar ajiya domin mu samu abun nan da muke so.
Mai yiwuwa kwarewa ne da muke yawan tunanin koyo. Ko kuwa wani riga da muka dade muke so. Koda menene, zamu iya amfani da fasaha mu ci nasarar burin mu.
Ga yadda zamu yi:
- Kudin cikin waya: Wannan na taimakan mu ajiya, da tura kudi, da kuma karban kudi a cikin wayan mu. Zamu iya siyan katin waya da kuma wasu abubuwa da zamu iya siya. Yana da sauri kuma da saukin amfani.
- Aikace-aikace na Kasafi: Akwai aikace-aikace da yawa a kyauta dake saka ajiya nishadi. Yaya? Idan kudin alijuhun mu na mako dubu daya ne, zamu iya jerin komai da muke so. Zai taimake mu shiri da kyau kuma mu maida hankali. A lokaci kadan zamu ajiyan kudi da yawa fiye da muke tunani.
Share your feedback