Meye kuke son ku zama?

Ku gano a matakai uku

Me kuke son ku zama idan kuka yi girma? Wannan na iya zama tambaya mai wuya, musamman idan baku san abun fadi ba.

Duk da haka, kada ku damu. Wadannan matakan guda uku zasu taimake ku. Kun shirya? Toh muje zuwa:

Kuyi tunanin abun da kuke son yi?
Yakamata aikin da kuke son kuyi ya zama wani abu da kuke son yi sosai. Saboda haka kuyi tunanin abubuwa da kuka fi so. Kuna son yin zane? Mai yiwuwa ku zama masu yin zane. Kuna son fadin labarai? Mai yiwuwa yin rubutu ne ya dace daku. Kun iya lissafi? Zaku iya zamu mai kasuwanci ko kuwa wande ke kula da harkan kudade wata rana.

Ku tambaye yan uwan ku abun da kuka iya yi sosai
Baku san ko menene kwarewar ku ba? Ba ku kadai bane. Kuyi magana da wadanda suka san ku sosai kamar yan uwan ku mata da maza da kuma abokan ku. Suna kaunar ku kuma suna goyon bayan ku. Saboda haka, zasu gaya mu gaskiya. Zasu iya taimakon ku sanin kwarewar ku kuma kuci nasara.

Kuyi binciken sabobin abubuwa
Ku bude idannun ku. Mai yiwuwa ku gano wani aiki da baku sani ba. Zaku iya koyan sabobin fasaha kamar tsarin dokokin kwamfuta da kuma zane hoto a kwamfuta. Akwai abubuwa da yawa masu nishadi da zaku iya gwadawa. Wa ya sani? Mai yiwuwa ku gano wani fasaha da baku san kuna da ba.

Idan kun san abun da kuke son ku zama a nan gaba, kun hadu! Idan baku sani ba tukun, kun hadu! Babu masu nasara da marasa nasara a nan.

Ku tuna, baza ku gano abun da kuke son ku zama a rana daya ba. Tafiya ce, kuma tafiya na daukan lokaci. Kuyi hakuri kuma ku bar abubuwa su zo muka a daidan lokaci. Idan kuka bi zuciyar ku, zaku fado a wajan daya kamata.

Kun san abun da kuke son ku zama idan kuka yi girma? Idan baku sani ba, zaku gwada wadannan matakan? Ku gaya mana a nan kasa.

Share your feedback