Wanda lokaci ne ya dace ayi aure?

Labarin Hauwa

Lokacin da nake shekaru goma sha biyu, mahaifi na ya aurar dani ma wani manomi dake da kudi da mata uku da ake kira Mallam Aminu.

Dana fara aure kusan kowane rana ina kuka. Nayi kewan iyali na, da abokai na da kuma makaranta. Na kasa fahimce dalilin da nake nan wajan. Ina bakin ciki.

Mai gida na ya hana ni zuwa makaranta.

yawwancin lokuta kawai zama nake yi a gida na lura da yan kankanin yaran.

Na san zan iya zama fiye da haka. Na tambaye mai gida na ko zai barni na koya wani sana’a ko kwarewa. Da farko yaki yarda amma dana roke shi. A karshe sai ya yarda.
v Nayi rijista da wani hadaddiyar kungiya dake koyars da yin dutsen ado a al’ummar mu. A wajan ne na hadu da wasu yan mata ma’aurata kamar iri na .

A wajan aka koya mana yadda zamu fara namu sana’ar da kuma yadda zamu tafiyad da kasuwancin mu bayan da muka cika samun horon mu. A lokacin samun horon na fara yin dutsen adon ma yaran gida da kuma sauran matan.
v Bada jimawa ba wasu mata suka fara biya na na yi musu dutsen adon. Bana dogara akan mai gida na domin kowane abu kuma.

Yanzu a shekaru goma sha takwas, ina da yaro guda kuma ina da kwarewa dake kawo mun riba da zan iya lura da kai na da mai gida na.

Mai gida na ya tambaye sauran matan suje su koya wani sana’a. Har ya fara karfafa gwiwan sauran yara mata su koma makaranta.

Mai yiwuwa ban iya cewa a’a ma aure da sauri ba amma nayi kokari na gyara rayuwa ta na gaba dana gida na kam kam

Kema zaki iya yin haka ma kanki.

Ana matsa miki lambar kiyi aure? Kina ganin baki shirya ba? Kada kiyi shiru. Kiyi wa wani babba da kika yarda da magana ko kuwa iyayen ki akan wannan. Ki gaya musu cewa baki shirya ba. Idan baki tabbata yadda zaki yi musu magana ki gwada yin wa wani ko wata yar dangantakan ku da kika yarda da. Zasu iya taimakon ki fara tattaunawa da iyayen ki.

Kin riga kinyi aure? Ba karshen rayuwar ki na gaba kenan ba. Kamar Hauwa wani abu mai kyau zai iya fitowa daga al’amarin nan. Idan baki fidda rai ba.

Share your feedback