Zaku iya cin nasara da kudi!

Yadda zaku yi ajiya da kuma samun kudi

Kasancewa mai iya rike kudi na nufi cewa kun san yadda zaku samu kudi kuma kuyi ajiya.

Wannan ba basira da ake haife ku dashi bane. Wannan kwarewa ne.

Abun dadin shine wannan kwarewa ne da zaku iya koya.

Idan kuka koya da wuri, zaku yi gwajin sa. Idan kuka yi gwaji sosai, zaku kware da yin sa.

Saboda haka ku fara tun yanzu, ga yadda zaku yi….

Ku siyar dashi
Idan baku bukatan sa, ku siyar dashi. Takardu, kayan wasa, takalma, kaya, da sauran su. Duk abun da kuke da da baku yi amfani da ba a shekara daya ko fiye da haka, toh mai yiwuwa baku bukatan sa.

Ku samu kudi a gefe
Kuyi amfani da kwarewar ku.
Mai yiwuwa yin cake ne, ko dinki, ko kuwa gyaran abubuwa a gidan makwaftan ku.
Hanyoyi da zaku iya kara samun kudi na ko ina. Ku duba kusa daku wa hanyoyi masu tsira da zaku iya samun kudi.
Zaku iya karanta wannan makalar akan hanyoyi da zaku samu kudi.
Kuyi hankali, mutane zasu iya gwada yin wa ‘yar mace mai neman kudi keta. Ku yarda da ilhamar ku, idan kuka ji kamar wani abu bai dace ba, toh mai yiwuwa haka ne. Kuyi magana da wani amintaccen mutum idan kuna ji kamar baku tsira ba.

Ku duba abubuwa a shaguna dabam-dabam
Kada ku siyo abubuwa a shagon da kuka fara zuwa. Ku kwatanta farashin a shaguna dabam-dabam kafan ku siya. Kada kuji tsoron yin farashi.

Kada ku kashe dukka kudin ku
Samun karin kudi baya nufi cewa ku kashe shi dukka. Kuyi ajiyar wasu. Yakamata kuyi ajiyar duk karin kudi daya rage daga siyan abubuwa mafi muhimmanci.
Idan kunyi kankantar bude asusuwan ajiya a banki, ku siya asusu a gida da makulli kuyi ajiyar kudin ku.

Zaku iya duba nana

Wanda hanyoyi ne kuma kuke tunanin zaku iya samun kudi? Rarraba da mu a sashin sharhi.

Share your feedback