Karfin ikon ku

Kun san cewa kuna da duka wadannan a cikin ku?

Sannu Yan Springster!

Zamu gaya muku wani babban sirri. Kun shirya? Toh gashi nan.

Kuna da “KARFIN IKO”. Eh gaskiya ne.

Mun san kuna al’ajabin yadda yan mata kamar ku zasu iya samun karfin iko?

Idan kuka karanta labaran mu na Springster koda yaushe kuma kuna kiran kanku Yan Springster, zaku samu daman samun wasu irin iko da zai baku karfin shawo yawancin matsaloli.

Kuna al’ajabin wadannan ikokin?.....

Karfin Iko na daya: Kuna da TABBACI
Kasancewa Yan Springster na baku dalilai dari da zaku yi imani da kanku. Idan kuka yarda da kanku, zai baku tabbacin da kuke bukata ku shawo kan matsaloli kuma ku jawo canji a al’ummar ku. Kada ku manta kuna da daraja kuma rayuwar ku nada muhimmanci. Zaku iya bude tabbacin ku ta yin imani da baiwan ku da kuma kwarewar dake cikin ku, yin aiki sosai, sai kuma amfani dasu domin ku taimake sauran mutane.

Karfin iko na biyu: Kuna da KARFI
Idan kuna ji kamar wani abu ba zai iya yiwuwa ba, ku tuna dukka gagaruman yan mata dake cimma burinsu a duke fadin duniya! Idan zasu iya yi, ku ma zaku iya yi. Saboda haka idan kuna masaniyar wani babban matsala, kada ku manta da karfin da kuke da, dake zuwa daga kasancewa mace.

Karfin iko na uku: Baku KADAI BANE
Idan abubuwa suka kasance da wuya, zaku iya neman goyon baya daga abokan ku, ko iyalan ku, da kuma sauran Yan Springster- Ba lallai sai kun bi da rayuwa ku kade ba. Zamu goya muku baya! Idan matsalolin ku suka sha karfin ku, neman taimako nada kyau!

Zaku iya farawa yanzu. Kuna bukatan taimako da wani matsala? Kuyi magana akan su da babban Yaya da sauran Yan Springster a sashin sharhi.

Share your feedback