Ki sa mahaifiyarki jin dadi ba sai kin kashe kudi sosai ba
A naijeriya ranar uwa na fadawa a watan maris, a rana ishirin da shida (26th, Maris). Mun san cewa kina nuna wa mahaifiyarki ko wanda yake duba ki (yar uwar mamanki ko mutumin dake tsaran ki) kauna a ko wanda rana. Wannan dama ne ki kara nuna musu kauna. Ga kyauta masu kyau guda biyar da zaki iya basu, ko da kasafin ki ba yawa.
Katin kwali da kika yi da kanki
Uwaye na jin dadi idan kika basu abu. Abunda kike bukuta kawai shine kwali ko fallen takada da kuma fensiri mai kalla na zane zane. Kiyi amfani da tunanin ki da kwarewan zane zane ki! Ki tabata cewa katin ya nuna yawan kaunan da kike mata.
Wasika
Rubuta mata wasika, ki gaya mata yadda kike kaunan ta. Ki amfani da hanun rubutun ki mai kyau. Ki tabbata kin nuna mata godiya da duka abubuwan da take miki. Zai nuna cewa kina kaunar ta sosai
Kiyi mata abinci/ki tsaftace gidan
uwaye na aiki sosai, da haka suna bukatan hutu. Mai yiwuwa kina da aike aike da kike yi a gida ko wanda rana. Ki bawa mahaifiyarki lokaci ta huta, sai ki mata aikin ta. Akwai abincin da take so? Ki koya yadda ake yin abincin sai ki bata mamaki ki dafa mata irinsa.
Ki rungume ta
Zaki ga kaman karamin abu ne, ama runguma na sa mutum jin dadi sosai. Zaki nuna mata yadda kike kaunar ta.
Hoto da kika yi da hanun ki
Ke da iyali ki ne abun muhimmanci a wajan ta. Hotunan ku tare zai kara mata farin ciki. Zaki iya yin hoton daga kwalin takada. Ki samu wani hoton ku mai kyau da zai shiga ciki. Kiyi wa hoton kwalliya da kalmomi da zane zane da zai nuna kina kaunar ta.
Ranar Uwa ba na Uwaye bane kawai. Zaki iya bawa wata babba dake duba ki.Zai iya zama mai koyar dake a makaranta, ko makwafciya ki, ko yar uwar mahaifiyarki. Ko waye ne zai so kyautan saboda yazo daga wajan ki.
Share your feedback