Labarai guda biyar maras tushe akan samarai

Ki samu asalin gaskiyn

Duk muna jin mutane na cewa “ “samarai, samarai ne basu canzawa”. wannan zai iya samu tunanin cewa duka samarai daya ne. Gaskiyar shine, yawancin samarai na nan kamar ki. Jikin su na canzawa tare da tunanin su. su ma suna girma.

Ga wasu abubuwa mai yiwuya da kike tunani akan samarai.

Samarai basu da kawazuci
"Ana raunata ni kuma wasu lokuta ina jin kamar zanyi kuka dan kawai na nuna fushi na. wasu lokuta idan na nuna shauki na mutane na ce mun na nuna halayya ta jinsin maza amma ina yauwan cewa nima mutum ne kuma ina da kawazuci". Adamu, 16

Samarai basu son ana kula da su
“ina son mutane su kula dani wasu lokuta. Ina son su bani lokutan su. Wasu lokuta ina yin abun da zai sa su kula dani. Nima ina son a bata ni. Ba mata ne kawai ke bukatan kulawa ba, muma maza muna bukatan wannan irin kulawar". Ahmed, 17

Samarai na tattare da matsala
“wata rana na lura cewa wata yarinya ta datti da kanyan ta da jini sai da sauri na bata riga na ta daure a kwan-kwason ta domin ta rufe dattin. Ya kamata namiji ya lura da mutane da suke kusa dashi. Dan haka, idan muka baku matsala, saboda mu kare mutanen da muke kauna ne. Bamu tattare da matsala ba". Mustapha, 15

Samarai ma na son su koyo
“ ina son na koya sabobin abubuwa. Shiyasa na koya yin girki. Ina jin dadi idan na koya sabobin bayanai yadda zanyi girki. Ko yan uwa na mata tare da mahaifiya ta sunce nafi su iya girki. Ina yawwan gaya musu cewa ba mata bane kawai ke koyan yi abubuwa". Umar, 15

Samarai baza su iya abokanta da mata ba
“Bansan dalilin da yasa mutane ke cewa maza da mata baza su iya abokanta ba. ina son abokanta da mata, suna bani shawara masu kyau, kuma suna da kirki. Ba ko wanda lokaci bane nake jin wasa da abokai na maza". Shehu, 16

Samarai zasu iya zama abokan arziki. Zaki iya koyan abubuwa da yawa daga wajan su. Zaki iya koya musu abubuwa ma. Mai kike gani? Gaya mana ra’ayin ki a shafin sharhin mu.

Share your feedback