Abubuwa guda biyar masu nishadi da kuma tsira da zaku iya yi da abokan ku

Yadda zaku yi nishadi a ungwan ku

Watan ranar yara a kasar Najeriya…..Madalla!!!

Kuna al’ajabin wani abun nishadi da zaku iya yi da abokan ku a ranar?

Akwai abubuwan nishadi da kuma tsira da zaku iya yi.

A nan kasa zaku samu jerin kadan;

Ku fara wani kungiya
Kuna son yin zane? Zaku iya yin zanen wani hoto tare da abokan ku. Ga misali, zai iya zama hotunan ku. Zaku iya rataya hoton a gidan ku domin ya tunatar muku da ranar da ku da abokan ku kuka kirkira wannan mafificcin abun.

Yin waka ko rawa
Kuna son yin rawa ko waka? Ku zabi wani waka ko wani rawa. Tare da abokan ku zaku iya nishadantar da iyalin ku ko kuwa sauran mutane da wakan ku ko kuwa rawar ku. Zaku iya hada wani gasar rawa ko waka da yaran ungwan ku. Wannan zai iya zama abun nishadi. Kuma zai iya zama wani hanyar samun sabobin abokai

Ku gwada wani sabon abu tare
Kun taba gwada yin wasannin bidiyo? Wa yace baza ku iya buga wasan kwallon kafa ko kwallon kwando. Tare da abokan ku zaku iya kalubale yan mazan ungwanku ku buga wasan kwallon kafa ko kuwa yin gudu. Zaku iya zuwa rairayin bakin teku da abokan ku.

Ku saka kai a wani abu
Ku da abokan ku zaku iya saka kai ku wanke motocin mutane a ungwan ku. Zaku iya ziyarta wani gidan marayu kuyi wasa da yaran wajan. Zaku iya sa kai ku gyara gidan wata tsohuwar makwafciyar ku. Wadannan zasu iya zama abubuwan nishadi. Gaskiyar shine, taimakon mutane zai saka ku jin dadi kanku. Wannan zai iya saka ku jin farin cikin sanin cewa kun saka wasu murmushi.

Ku kalla wani fim tare
Ku kirkira naku gidan kallon a gidan ku. Ku zabi fim din da zaku so ku kalla. Ku zabi gidan wa zaku je ku kalla. Ku siya guru-guru ko biskit domin ku samu ku motsa baki idan kuna kallo. Ku tabbata kun samu izinin wata/wani amintaccen babba a gida kafan ku gayyece abokan ku. Zaku yi nishadi idan kuka shirya da kyau.
Kuma zaku iya kirkira naku wasan kwaikwayo domin wasu su kalla. Ga misali, ku da abokan ku zaku iya kirkira wani wasa daga wani takarda da kuka karanta ko wani sanannen labari.
Zaku nishadantar mutane dake kusa daku, kuma Ku ma zaku yi nishadi . Mai yiwuwa ma ku nemo wani boyayyen kwarewa da baku san kuna da ba.

Ku gwada wasu dabarun mu sai ku gaya mana yadda kuka ji payan da kuka gwada su.

Kuna da wasu dabaru akan yadda zaku yi nishadi kuma ku tsirata kanku da abokan ku? Ku rarraba damu a sashin sharhi.

Share your feedback