Bai kamata ‘yar mace ta zama baiwa ba

Wata yarinyar mai shekaru goma sha bakwai ta ci nasarar samun lambar girmamawa da ake kira Nobel Peace Prize!

Malala Yousafzai da shekaru goma sha bakwai daga Jihar Pakistan ta shiga tahiri da ta zama karama mai nasarar Nobel Peace Prize- Wani lambar girmamawa ne wa mutane da suka yi aiki mai inganci.

Shekarun Malala goma sha daya da ta fara yin magana akan hakkin ilmin yan mata.

Da take shekaru goma sha biyu wasu maza suka so su kashe ta.

Suna son ta daina fada akan ilmin yan mata. Amma ta ki bari kuma duk da haka masaniyar ya kara karfafa ta, ya cire mata tsoro kuma ya kara kudurta ta.

Data karbi lambar girmamawar ga abubuwan da ta fadi “Wanna abun ya karfafa ni naje gaba kuma na imani da kaina. Yana da kyau a san cewa mutane na goyon baya na. Muna nan tare.”

“Ina godiya ga mahaifina da bai hana ni ba; daya bar ni na cimma buri na. Daya nuna wa duniya cewa bai kamata ‘yar mace ta zama baiwa ba.”


Mahaifin Malala mai sunnan Ziauddin Yousafzai yace yana fatan wannan lambar girmamawan zai taimake hakkin yan mata a ko ina.

Kamar Malala kuma zaku iya tsaya wa wani hakki yau. Zaku iya zama wani misali da wasu yan mata zasu iya bi.

Mutane zasu so su tsorata ku daga bin muradin ku. Zasu so su saka ku ji kamar bai kamata ku cimma babban abubuwa ba.

Kada ku bari ayukan su ya hana ku.

Saboda yan mata, kun fi abun da suke tunani. Ku gagarumai ne.

Zaku iya cimma kowane abu da kuke so.

Abun da kuke bukata shine yin imani da kanku, kudurta da kuma aiki domin kuci nasara.

Kamar Malala ku sami wani amintaccen mutum da zai shawarta ku ko kuwa ya ja gora ku.

Kun san wata kamar Malala a al’ummar ku? Kuyi mana magana akan ta a sashin sharhin mu.

Share your feedback