Zaku yi tafiya a wannan lokacin bukukuwar?

Yadda zaku yi tafiya mai lafiya da kuma nishadi

Wannan shekarar na zuwa karshe. Wa wasu wannan yana nufin abinci, bukukuwa da kuma nishadi.

Wa wasu kuma, yana nufin lokacin yin tafiya. Mai yiwuwa da iyali ko kuwa abokai. Mai yiwuwa a motar gida ko kuwa motar haya.

Duk yadda ya kasance, muna son kuji dadin tafiyar ku kuma ku tsira.

Mun hada dabaru akan yadda zaku yi tafiya mafi kyau.

Kuyi caji da kuma saka kati a wayoyin ku
Kuna da waya? Kuyi cajin sa da kyau a cikin dare kafan tafiyar ku.
Baku san lokaci da kuma inda maiyiwuwa zaku bukatan yin waya ba. Ku tabbata kun siyo katin waya.

Ku tattara kayan nishadin ku
Zaku iya kwashe kwalin katuna, ko ludo da sauran su.
Kuma zaku iya yin wasan makin alamomi kan hanya.
Duk wanda yafi yin makin alamomin a karshen tafiyar zai zama mai nasara.

Ku kwashe wasu wakoki
Zaku yi tafiyar a motar gida ne? Ku dauke wannan faifan wakokin da kuka fi so daku. Zaku iya kuna yin wakoki tare da iyalan ku. Zaku yi tafiyar da motar haya ne? Ku dauke wani faifai ko kuwa rediyo daku, ko ku tabbata wayar ku nada wakoki sosai.

Ku dauke hotuna
Kuna da na’urar daukar hoto ko kuwa waya mai daukan hoto? Ku dauke hotuna.
Ku dauke hotunan kanku ko wani abu da kuka gani a hanya. Zai iya zama masu talle dake bin motoci a hanyar Kano ko kuwa masu siyar da manja a hanyar Zaria, da sauran wajaje. Zaku iya rarraba hotunan a Facebook ko kuwa wannan shafukan sada zumunta da kuka fi so.

Ku kirkira wani masaniya wa kanku a lokacin tafiyar ku. Kada kuyi bacci kawai a dukkan tafiyar ku. Ku tuna ku tsirata kanku kuma ku kula da muhallin ku a koda yaushe.

Zaku yi tafiya wannan shekarar? Ina zaku je? Menene kuka tsara zaku yi a wannan lokacin bukukuwar? Kuyi mana magana a wajan sharhi.

Share your feedback