Hanyoyi guda huda da zai taimake ki zama mutum da ake girmama a al’umman ku

Baki kankantar wa mutune su girmama ki ba

kina ganin kin kankanta ki zama misali wa mutane a al’ummar ki? A’a. Akwai abubuwa da yawa da yan uwan ki, ko abokai ki da yan makwaftar ki zasu iya koya daga wajan ki.

Ga wasu hanyoyi da zaki iya zama mutum da ake girmamawa.

Ki samu tabbataccen hali
Idan kina da tabbataccen hali, zaki riga kallon rayuwa a yankin haske. Zaki kokarin zama cikin farin ciki da murmushi. Idan abubuwa suka je ba daidai ba zaki kokarin mai da hankali akan abun da zaki iya yi dan ki mai da shi mafi inganci. Baza ki cire rai ba. Kin yarda cewa kina da ikon mai da burin ki ya zamo gaskiya. Wannan misali mai kyau ne da zaki nuna wa kannan ki.

Ki girmama na gaba dake
Girmama na gaba dake na nufin cewa kina da tarbiyya da hali mai kyau. Yana nufin bi da mutane da kyau. Abun muhimmanci ne ki girmama wanda suka girme ki da wanda kika girma. Baya nufin cewa kiyi komai da suka gaya miki. Idan kika ji kamar babu kyau, zaki iya cewa a’a. Yana da muhimmanci ki girmama kanki. Idan kina da tarbiyya mai kayu, iyaye zasu so yaransu su zama kamar ke.

Ki zama mai koyarwa
Ba sai kinyi aiki a makaranta ba kafan ki zama mai koyarwa. Ki rarraba abubuwan da kika koya. Wani abu daga wannan shafin yanar gizo gizon zai iya taimakon wani abokin ki. Zaki iya koyan wani abu daga makaranta da zai iya taimakon makwafcin ki.

Ki zama mai taimako
Ki hade da wani kungiya dake taimakon mutane a al’ummar ki. Ko kuwa a majami’a ko masallacin ki. Ki tabbata kinyi wa wani babba da kika yarda da magana tukun, saboda ki zabe hanyar mai sauki da zaki iya taimako. Zaki iya isar da sako wa manyan da suke farfajiyar gidan ku ko kuwa ki taimaka yan uwan ki yin aikin makarantar su.

Babu wuya ki zama wanda za’a girmama. Zai dauke karamin aiki ne kawai. Ba zai yi kyau ki samu mutane dake girmama ki ba? Kina da wani da kike girmamawa a al’ummar ki? Ki gaya mana akan su a shafin sharhin mu.

Share your feedback