Ki samu lafiya, ki samu farin ciki

Kada ki bari girman jikin ki ya shafi farin cikin ki

Nassan yadda zaki ji idan aka kira ki mai kiba

Ina da katon ciki, wasu lokaci abokai na namun dariya idan na sa matsatstsen kaya.

Wasu mutane sunce na daina cin abinci sosai. Wasu kuma sunce na fara atisaye.

Nayi tunanin shan kwayar maganin rage kiba. Ina ganin tallace tallace a ko ina. Na tabbata kema kina gani. Ance idan kika sha wannan kwayar magani keman zaki zama kaman yan matan nan na saman jarida a kwanaki kadan. Abunda basu fadi shine, wadannan kwayar magani ko shayi basu cika aiki ba. Wasu lokaci ma zasu iya ja miki lahani.
v Bazan iya hana ki ba idan kika yanke shawara cewa zaki Gwada wadannan kawyar maganin ko shayin. Idan kika yi, dan Allah ki tabbata kin tsirar da kanki.

  • Ki tabbata kin yarda da mutumin dake siyar da kayan nan
  • Ki duba ko da me ake yin sa. Koda sanfurin kayan sannane ne. Yana da muhimmanci. Ki san mai kike sha.
  • Ki bincika a yanar gizo gizo akan tasirin Abunda kike son ki sha. Baza ki so kiyi rashin lafiya ba a maimakon rage kiba.
  • Kiyi magana da likitan ki wanda kika yarda da. Suna son su tabbata cewa kina da lafiya. Zasu gaya miki gaskiya akan abunda zai miki aiki da Abunda ba zai yi ba.

Gaskiyan maganan shine kiji dadi da yadda kike. Kada ki yarda abubuwan da mutane ke fadi akan jikin ki ya tura ki daukan wani mataki akan jikin ki da zai saki da na sani nan da gaba.

Abun muhimmancin shine kina da lafiya kuma kina cin abinci masu kyau kuma kina yin atisaye.

Ki samu farin ciki da kanki kuma ki samu hanyan yin atisaye. Nasan bai da sauki kaman shan kwayar magani, amma babu kwayar magani mai inganci kaman kaunar kanki.

Share your feedback