Babban Yaya ina bukatan amsa

Kuyi magana da Babban Yaya akan komai da komai

Sannu ‘Yan Springster,

Mun san kuna wannan lokaci da kuke son ku san abubuwa da yawa.

Mai yiwuwa kuna da tambayoyi kuma baku da wanda zaku tambaya.

Mai yiwuwa kuna jin kunyar tambaya. Baku son kowa ya hukunta ku.

Kuna son wani da zai saurara ku. Kuna son wani ya baku shawara.

Kun san mene? Babban Yaya na nan ta taimake ku. Tana son ta amsa tambayoyin ku.

Tana son ta saurare ku idan kuna maganar abokan ku, ko samari, ko jikin ku, ko balaga, kayan yayi, da komai.

Tana son ta amsa tambayoyin ku. Ta taimake ku kawar da dukkan shakkar ku akan wasu abubuwa.

A mako na gaba Babban Yaya zata dauke rana guda domin ta amsa wasu tamboyin ku a wani makala.

Kuna son Babban Yaya ta amsa tambayoyin ku a makalar ta na gaba? Ku rarraba tambayoyin ku da mu a wajan sharhi a nan kasa.

Ku hade damu a mako na gaba da Babban Yaya zata amsa tambayoyin ku.

Share your feedback