Kun iya wannan wasan?

Baku tsufa kuyi nishadi ba

Zaku iya tuna da wasan yar gala-gala ko kuwa suye?

Toh, wa yace kunyi tsufa kuyi wasannin nan yanzu? Kun san ba wanda ya tsufa yayi nishadi ko?

Mun san yanzu kuna son ku kwashe lokaci da abokan ku da kuma haduwa da sabobin abokai. Amma, idan muka gaya muku cewa yin wasanni wani hanya ne da zaku yi nishadi, kara shakuwa da abokan ku, da kuma samun sabobin abokai fa?

Banda nishadi, yin wasannin na kara ilmi ma. Zamu iya daukan wani kwarewa daga yin wasanni. Kwarewa kamar shawo kan matsala, daukan shawara, da kuma kwarewar yin abubuwa da yawa a lokaci daya.

Yin wasanni hanya daya ne da zaku inganta kwarewar ku da kuma natsuwar ku.

Kun shirya yin nishadi? Ku duba wasu wasanni da zaku iya gwadawa da abokan ku;

Wasan ten-ten

Kuna neman wani abu da zai taimake ku motsa jiki. Ku gwada yin wasan yar gala-gala. Zai taimaka kara halin iya jurewar ku. Kuma wannan wasan zai taimake ku koyan yadda zaku yi tunani da sauri. Wani abu da dukkan mu ke bukata a rayuwa.

Ludo

Wannan wasan zai iya taimaka ya bunkasa kwarewar ku na ilmin lissafi (wato ikon yin lissafi). Kuma zai koya muku yadda zaku zama masu yanke shawara masu kyau da kuma yadda zaku bi da matsin lamabar.

Wasan kati (WHOT)

Wannan wasan zai bunkasa kwarewar ku na yanke shawara. Kuma zai taimake ku tunani da sauri da kuma zama masu kiyayewa. Wasannin kati zai taimaka inganta ikon yin tunani.

Wasan buya

Wannan wasan zai taimake ku bunkasa kwarewar ku na shawo kan matsala. Kuma zai taimaka inganta tunanin ku, saboda haka, kwarewar ku zai karu.

An kusa ayi hutu. Wana wasanni ne zaku so ku gwada? Wana sauran wasanni ne kuka sani? Ku rarraba damu a sashin sharhi.

Share your feedback