Ku yabe kanku

Kada ku jira wani ya yabe ku

Kun san wanda zaku yabe? Iyalai ku da kuma kowane mutum na musamman a rayuwar ku. Amma kun san wanda bai kamata ku mance kuyi wa yabo? Kanku? Meyasa? Saboda kun cancanta. Kuma baku bukatan kowa ya muku.

Saboda haka kada ku hana kanku. Ku yabe kanku koda yaushe. Kuna al’ajabin yadda zaku fara? Ga wasu dabaru.

Ku dauke minti daya
Ku dauke dan lokaci ku yabe abubuwan da kuka cimma. Zai iya zama kowane abu. Mai yiwuwa kun gano wani safga mai nishadi. Ko kuwa kun karasa kammala wani takarda mai dadi. Ko kuwa kun ci nasara a wani jarabawa. Koda wani hali ne da kuka daina. Koda menene, ku ja nunfashi ku amince da shi. Kuyi wa kanku godiya domin nasarar da kuka samu. Ku tsaya a gaban madubi kuce wa kanku “ Sannu da aiki, yarinya. Kin hadu!”

Kuyi wani abu da zai kawo muku farin ciki
Idan kuna son yin gudu, kuyi sa. Idan kuna da wakan da kuke so, ku ji sa. Idan kuna son daukan hotunan kanku, ko kuwa hotunan abokan ku, kuyi sa. Idan kuna son ku yabe kanku, kuna bukatan yin wani abu da zai kawo muku farin ciki. Shine abun muhimmanci.

ku bawa kanku lada
Idan zaku iya, ku bawa kanku wani abu da kuke ta son samu. Ba sai kun siyo wani abu ba. Zai iya zama wani abu mai sauki kamar tashi daga bacci da lati. Ko kuwa ziyarta Innar ku da kuka fi so. Wasu lokuta yan kananan abubuwan nan ne ke kawo farin ciki.

Ku karbi yabo
Idan wani ya fadi wani abu mai hankali akan ku, kada kuyi jayayya dasu. Kada kuji kunya ko kuwa ku damu ko suna fadin gaskiya ne. A maimako, kuce “kun gode” kuyi farin ciki. Zaku kara jin dadi. Kuma babu komai da wannan. Yana da kyau ku san yadda kuke da musamman.

Ku rubuta wa kanku wasika
Mai yiwuwa kun taba rubuta wa mutanen da kuke kauna wasika. Yanzu ku rubuta wa kanku. Ku rubuta dukkan abubuwan da kuke godiya da kuka cimma. Ku rubuta dukkan dalilan da yasa kuke kaunar kanku. Idan baku son ku rubuta, kuyi zane! Sai duk sanda kuke jin bakin ciki, ku karanta wasikar ko kuwa ku kali zanen kuma. Zai kara saka ku tabbaci da kanku kuma ya karfafa ku fiye da yadda kuke tunani. Zaku shirya ku mamaye duniya. Ku gwada yi yau.

Ya kuma kuke yaben kanku? Ku gaya mana a sashin sharhi.

Share your feedback