Sannu Mujalla, ni ce kuma
Ku bayyana ra’ayin ku da kuma yadda kuke ji
Kun san wani abun mamaki game da shekarun ku na matasa? Zasu kare da sauri fiye da kuke tunani. Daga masu kyau da mara kyau zuwa ko daya daga cikin su, duk zasu kare da wuri. Saboda haka, ajiye mujalla nada kyau.
Ba taimakon ku tuna masaniyar ku da shaukin ku kade yake yi ba. Yana kuma taimakon ku kara sanin kanku da kuma zama masu tabbaci. Kuma idan kuna son ku zama mawallafa, mujalla waje ne mai kyau da zaku fara. Ga yadda zaku yi:
- Ya zama mallakan ku: Na farko, ku samu wani takarda da ba’a amfani da. Sai ku rubuta sunan ku, shekarun ku da kuma safgar ku a shafi na farko. A ta nan, idan mujallar ku ya bace, zai yi muku saukin samuwa.
- Ku zabi wani tsarin aiki: Ku yanke shawara ko kuna son kuyi rubutu so daya a rana ko kuwa so daya a mako. Idan kuna son kuyi da safe, ba komai. Idan kuma zaku fi so kuyi sa da dare ne, ba komai. Koda yaushe ku fara da rubuta kwanan da kuma lokacin a saman shafin. Ku hada da sauran bayanai domin ku tuna da inda kuke a lokacin. Saboda a nan gaba idan kuka karanta mujallar ku, zaku tuna duk abubuwan da kuka koya, kuma ku rungume kanku mafi tabbaci.
- Kuyi rubutu: Ku dauke alkalamin rubutu sai ku fara aiki. Kuyi rubutun kamar kuna magana da kanku ko kuwa kuna labari da abokan ku. Kuyi rubutu akan kowane abu: yadda ranar ku ya kasance, muradin ku, tunanin ku mafi kyau, babban burin ku. Kada ku boye komai, yan mata. Ku fadi gaskiya. Ku tuna, ba komai idan kuka tsallake rana daya ko biyu. Kawai ku fara kuma daga inda kuka tsaya.
- yi masa kwaliya: Ku saka hotunan ku, kyallen kaya da kuma fure a cikin mujallar ku. Ku rubuta wakokin da kuke so, ruwaito da kuma kalmomin dake cikin waka. Ku rubuta wasu kalmomin yabo da aka gaya muku. Duk sanda kuke bakin ciki, ku duba wadannan kalmomin sai kuyi farin ciki.
- Ku tsare shi: Mujallar ku sirrin ku ne. Mallakan ku ne; saboda haka koda yaushe ku tsare shi a waje mai kyau. Ga misali, a tsakanin kayan ku da aka nannade, a cikin rigan matashin ku, har a karkashin wani kujera ko tebur.
Toh gashi nan! Kun shirya fara naku mujalla. Kuji dadin sa!
Kuna da mujalla? Ku gaya mana a sashin sharhi. Zamu ajiye sirrin ku.
Share your feedback