Kuna ji kamar ba mai goyon bayan ku?

Ga yadda zaku jimre

Wasu lokuta zamu ji kamar bamu cikin wani kungiya ko kuwa wani taro. Bamu da abokan tadi. Bamu da iyali da zamu kwashe lokaci da.

Akwai wasu lokuta da muke da mutane kusa damu amma muna jin kadaici.

Muna ji kamar mutanen dake kusa damu baza su fahimce mu ba.

Zamu fara gujen mutane. Zamu koma jin kadaici.

Kuma mun san babu wanda ke son jin haka.

Kuna al’ajabin yadda zaku kawar da yadda kuke jin kadaici?

Ga wasu dabaru:

Ku kewaya kanku da abokai da kuma mutane masu kaunar ku
Ku samu mutane a rayuwar ku da zaku iya yin wa magana akan kowane abu. Zai taimake ku jimre da kadaicin. Ku samu abokan arziki. Zaku iya samun abokai a wajan sujadar ku, ko a kungiyar goyon bayan ku, ko kuwa ku tambaye wani amintaccen mutum ya gabatar daku a wajan wata tsarar ku. Kuma zaku iya karanta wannan makalar akan yadda zaku samu abokai

Ku nemo ko kuwa ku shiga wani kungiya a al’ummar ku
. Zai iya zama wani kungiya mawaka, ko kungiyar yin rawa, har da kungiyar wasanin motsa jiki. Mai yiwuwa kuna son wasanin motsa jiki, zaku iya ziyarta wani cibiyan wasanin motsa jiki dake kusa daku. Kwashe lokaci kuna wasan da kuke so sosai zai saka ku jin dadi.
Mai yiwuwa kuna son yin rawa, zaku iya shigan wani kungiyar yin rawa. Zaku iya shigan wani al’ummar shafin yanar gioz gizo kamar Springster a Facebook. Shigan wani gungiya zai sa ya yiwu ku hadu da sabobin mutane.

Ku koya wani sabon abu mai nishadantarwa
Zai iya zama yadda ake buga ganga, ko yin ruwa, ko waka, ko kuwa burodi, da sauran su. Wannan zai iya zaman safgar ku. Zai taimake ku kwashe lokacin ku da kyau.

Duk abun da zaku yi, ku tuna cewa ba ku kadai bane. Zamu goya muku baya.

Kun taba jin haka? Ku gaya mana abun da kuka yi domin ku inganta yadda kuke ji a wajan sharhi.

Share your feedback