Yana son ki?

Bara mu taimake ku karanta wadannan alamun

Kuna zama cikin dare kuna tunanin wani? Kuna al’ajabin ko yana tunanin ku? Dukkan mu mun taba samun kan mu a cikin irin wannan al’amarin. Abu ne da aka saba dashi idan ana girma kuga mace ta fara tunanin samari. Wannan na cikin yanki a balaga.

Yana yiwuwa ku sani idan wani namiji na son ku. Wata rana muka jiyo Sarah da Ikenna na magana. Abubuwan da Ikenna ke fadi ya saka mu tunanin cewa yana son Sarah. Ga wasu daga cikin maganan su;

Ikenna– Kai Sarah, kin canza irin tsarin gashin ki. Ina son wannan “dukka bayan”. Nafi son sa fiye da “Shukun” nan da kika yi a lokacin daya wuce. *

Sarah– Nagode! Mun dade da ganin juna. Ikenna– Eh, gaskiya mun dade. Na bawa babban abokina labarin ki jiya. Na gaya masa cewa na dade da ganin ki.

Sarah– Akwai sabon labari?

Ikenna– Babu fa. Ina kallon wannan wasan kwaikwayon nan da kike magana akai. Ina son sa! Zamu iya kallon na gaba tare?*

Meyasa muke tunani Ikenna na son Sarah?

  1. Idan namiji na lura da bayyanar ki sosai, mai yiwuwa yana son ki. Musamman idan ya tuna da yadda kamanin ki daya wuce yake. Ikenna na lura da dukkan irin tsarin gashin Sarah.
  2. Idan namiji ya gaya wa abokan sa akan ki, mai yiwuwa yana son ki. Yana gaya wa abokan sa saboda yana son ki hadu dasu. Ikenna na gaya wa babban abokin sa akan Sarah.
  3. Idan namiji ya tuna abun da kike fadi, wannan wani alama ne. Ikenna ya tuna da wasan kwaikwayon nan da Sarah ke so. Ya nemo sa kuma ya fara kallo. Yana son abun da Sarah ke so.
  4. Kuma, Ikenna na son ya kalla wasan kwaikwayon tare da Sarah. Namijin dake son ki zai bada shawarar abubuwan da zaku iya yi tare.

Mu kuma mata fa,? Menene muke yi idan namiji na son mu kuma muna son sa? Zaku iya fadin gaskiya. Idan ya saka wani riga mai kyau, ku gaya masa. Idan kun iya wani darasi sosai, ku taya koyar dashi. Da kadan kadan, zaku kara sanin juna. Idan baku shirya yin soyayya ba, zai iya zama abokin ku kawai.

Idan baku son wani yaro, kada ku wayance kamar kuna yi. Ku gaya masa cewa shi mutumin kirki ne (Idan da gaske yana da kirki) amma baku kaunar sa haka. Kuyi tauri domin ya san kuna tsanani. Bayan nan ne zai kama hanyar sa.

Kuna da labarai akan maza dake son ku? Gaya mana a wajan sharhi.

Share your feedback