Ku nema naku “Babban Yaya”

Ku hade da wata gagarumar mace

Duniya zai iya kasance da wuya wa yan amata. Saboda haka yana da muhimmanci wa yan mata su goya bayan juna- shine abun da muke yi kowane lokaci a nan Springster.

Kuma kun san cewa duk sanda kuka zo kan Springster akwai wani abu na musamman a nan….babu kamar irin ta, Babban yaya!

*Buga kidin ruwa

Tana sauraren mu kuma bata bi damu kamar yara. Tana goyon bayan mu koda yaushe. Shiyasa muke girmama ta a kowane lokaci.

Amma bayan duk wannan, Springster ba shi kadai bane wajan da akwai wannan gagarumar macen. Akwai “Babban Yayi” da yawa da zaku iya haduwa da a can waje. Abun da kuke bukatan yi shine tuntuban su. Zaku yi mamakin abubuwan da zaku koya daga wajan su. Kuna al’ajabin yadda zaku fara? Ga wasu dabaru:

  1. Ku nema wani da kuke sha’awa: Ku duba kusa da ku; cikin iyalin ku, ungwan ku, al’ummar ku. Ku ga ko akwai wata budurwa dake yin wani abu da kuke sha’awa. Sai idan kuka san wata dake abokantaka da ita, ku tamabaya karin bayani akan ta. Ga misali, ya take? zata yi sha’awar shawarta ku? Kuyi kokari kada ku tambaya tambayoyi da basu dace ba. (Ga misal, zamu iya haduwa kowane mako?). Zai iya canza mata ra’ayin taimakon ku.
  2. Ku samu wata ta gabatar daku: Idan kuna son abubuwan da kuka ji game dasu, ku tambaye abokan ku su gabatar daku. Su san cewa kuna son su shawarta ku ne. Abokan su zasu mika sakon ku. Idan bata da matsala da wannan, za’a hada ganawa. Ku tuna, ku hadu a wajan jama’a. Ku kwantar da hankalin ku; komai zai kasance da kyau. Ku gaisa da ita sai ku gaya mata sunnan ku, kuyi fara’a da ladabi. Idan kuna tsoro, kuyi gwaji a gaban madubi kafan ku hadu dasu.
  3. Ku bar abubuwa su kasance da kan su: Bayan wannan haduwar na farko, ku dakata kuga yadda abubuwa zasu kasance. Komai zai kasance da kyau da dan lokaci. Ku cigaba da kwashe lokaci dasu a cikin jama’a. Ku cigaba da yin magana da su kuma da kara sanin su. Kada ku basu bayannan ku nan take. Ku tabbata duka abubuwan da kuka ji akan su gaskiya ne. Ku jira sai kun kara yarda da juna gabadaya. Sai ku dakata ku bar abubuwa su faru.

* Akwai wata “Babban Yaya” a rayuwar ku?

Menene wannan abun da kuke so game da ita? Ku rarraba da mu.

Share your feedback