Dalilai guda biyar dake fadin cewa kuna da ban mamaki

Yana cikin ku!

Tunanin ku (2)

Kun taba ji kamar baza ku iya cimma burin ku ba?

Eh, zaku iya! Kada ku bari wani ko kowane abu ya gaya muku wani abu dabam.

Abun shine, samun tabbaci a kanku nada muhimmanci. Zai taimake ku a rayuwa. Zai tura ku ku cigaba da kara kokari a al’amurra masu wuya, musamman idan kuna so ku fida da rai.

Akwai abubuwa da yawa da zaku iya yi domin ku gina tabbacin ku. Kamar karanta wannan makalar Springster akan yadda zaku zama masu tabbaci. (http://ng.heyspringster.com/sections/my-life/five-ways-be-more-confident/)

Amma kun san wani hanya mai kyau da zaku kara zama masu tabbaci? Kuyi imani da kanku! Saboda kuna da ban mamaki a yadda kuke. Ga dalilai guda biyar:

  1. Kuna da buri: Idan kuka yin sha’awar gina tabbacin ku, yana nuna cewa kuna da buri. Kuma wannan nada kyau.
  2. Kuna da karfi: Kunyi masaniyar lokuta masu kyau da kuma wasu mara kyau. Kuma kun fita da nasara.
  3. Kuna da jarunta: Kasancewa da tabbaci baya nufin cewa kun daina jin tsoro. Yana nufin cewa zaku iya yin karfin hali ku cimma burin ku.
  4. Kuna da hikima: Kun tuna wadannan lokutan da kuka shawo kan matsaloli masu wuya da kanku? Sai da wayo za’a iya yin wannan.
  5. Ku na musamman ne: An halice ku daidai da kuma kyau. Babu wata kamar irin ku a duniya. Eh, ku!

Toh ga wani aikin horo da zaku iya yi da wuri. Ku rubuta abubuwa guda uku da kuke so game da kanku. Mai yiwuwa kun iya aikin hannu. Ko kuwa kun iya saka mutane dariya. Ko kuna da hankali.

Kowane mako, ku kara rubuta wani abu daya. Ku cigaba da kara abubuwa. Sai duk sanda baku jin dadi, ku karanta shi ku tuna cewa ku gagarumai ne.

Menene wasu abubuwa dake saka ku kasancewa gagarumai? Fada mana a nan kasa.

Share your feedback

Tunanin ku

a yana da kyau

March 20, 2022, 7:54 p.m.

Latest Reply

Sannu yarinya! An rubuta wannan makalan saboda ke ne kuma muna farin ciki cewa kina son shi. zaki iya rarraba da abokai ki.