Abubuwa guda biyar da mai yiwuwa baku tsammanin zaku iya yi da waya ba

Abun ban mamaki a hanun ku

Yin kira, yin tadi, yin sakon rubutu. Abubuwa guda uku masu nishadi da kuke yi da wayoyin ku kowane rana. Amma zaku yi mamakin yadda zaku iya yin abubuwa fiye da haka. Abu mafi burgewar shine, baku bukatan wayar komai da ruwanka domin kuyi wasu abubuwa. Koda karamin waya ne, zai yi amfani. Kun shirya? Mu fara:

  1. Kuyi setin naku burin: Kalandar waya nada kyau. Zasu iya taimakon ku cin nasarar duk abun da kuke so. A ce kuna ajiya wa wani riga, kuma kuna son ku siyo shi a wani takamammen rana. Zaku iya rubuta shi a kalandar ku, sai kuyi makin ranar domin ku maida hankali. A lokaci kadan zaku fara makin buri fiye da kuke tunani.
  2. Ku lura da al’adar ku: Akwai aikace-aikace na kyauta akan lura da al’ada da zai iya taimkan ku. Domin farawa, kuje wani ma’ajiyar aikace-aikace kamar google play ko kuwa ma’ajiyar aikace-aikacen Opera. Ku bincika aikace-aikacen lura da al’ada sai ku saukar dasu zuwa wayan ku. Zai lissafa al’adar ku kuma ya nuna muka lokacin da zaku fara al’adar ku na nan gaba. Kuma idan kuna amfani da wayar da wani ne, zaku iya kirkira wani lambar sirri domin sirrinku. Baku da wayar komai da ruwanka? Duk da haka zaku iya lura da al’adar da kalandar wayar ku. Kuyi makin ranar farkon al’adar ku. Sai ku kola da ranar farkon al’adar ku guda biyu a nan baga. Ku kirga yawan kwanaki daga farkon al’ada daya zuwa na gaba. Idan kuka kirga kwanaki ishirin da takwas, toh wannan yana nufin cewa mai yiyuwa al’adar ku na nan gaba zai fara a kwanaki ishirin da takwas bayan ranar farkon al’adar ku daya wuce. Kuyi setin wani tunatarwa a kalanda saboda kada ku manta.
  3. Ku toshe bugun waya da kuma sakon rubutu: Kun san wannan yaron da yaki daina kira ko tura sakon rubutu bayan kun gaya masa da hankali ya daina? Ku toshe shi ta hanyar zuwa wajan setin wayar ku sai ku bi matakai nan masu sauki da aka jera. Kwanciyar hankalin ku yazo farko koda yaushe.
  4. Motsa jiki: Yawancin wayar komai da ruwanka nada aikace-aikacen motsa jiki da zasu taimake ku kola da siffar ku. Amma yan kananan wayoyi ma zasu iya yin amfani. Idan kuna son ku sha ruwa sosai kowane rana, zaku iya fara wani mujallar waya domin ku dubu matsayin da kuka kai. Zaku iya rubuta abun da kuka ci, kola da abinci mai kyau da mara kyau zai taimake ku ganin inda zaku canza dabi’ar ku domin ku fara daidaita cin abincin ku. Idan kuna da Jiki mai isashshen lafiya, zaku samu farin ciki.
  5. Kuyi wasanni: A nan gaba idan kuna gundura, ku dauke wayanku ku buga wasa. Daga kasada zuwa wasanin gwada ilmi, hanyoyi ne masu kyau da zaku walwala kuma ku koya abu daya ko biyu.

Da kuke koyo akan wadannan abubuwan masu kyau, ku tuna cewa ku Springsters ne sai ku “Rarraba kauna”. Gaya wa abokan ku akan wadannan sidabbarun ta yin tadi, da rabo a shafukan sada zumunta, da kuma tura hotuna.

Akwai abun da bamu fadi ba? Gaya mana a wajan sharhi.

Share your feedback