Hanyoyi guda biyar da zaku guje abokai mara kyau

Ku fuskanta rayuwar ku kuma ku cigaba da tafiya da karfi

Abokantaka kyauta ne mai ban mamaki. Yana saka rayuwa tayi kyau a hanyoyi da yawa. Amma wasu lokuta, muna ganewa cewa “abokai” ba komai bane.

Suna saka mu jin wani iri kuma su zage mu. Suna yin maganar mu a bayan mu. Basu son cigabawar mu.

Ana kiran wannan, abokantaka mai guba. Bashi da kyau wa kowane mutum. A irin wadannan al’amurrar, yana da kyau ku kashe abokantakar. Ku sake wannan “kawar” domin ku fuskanta rayuwar ku na gaba.

Yanke mutum daga rayuwar mu ba abu mai sauki bane. Amma zai iya aukuwa.

Ga yadda zaku yi:

Ku tabbata
Na farko, ku tabbata cewa baku son ku zama abokai da mutumin nan kuma. Babu wanda ya cika goma. Kada mu sake wata “kawar” mu domin sun raunata mu so daya. Amma idan suka yi so dayawa, yana da kyau mu yanke abokantakar. Muyi kokari kada muyi bakin ciki. A maimako, muyi tauri. Dukkan mu na cancantar farin ciki.

Ku fuskanta juna kuyi Magana
Ku zauna kuyi magana. Ku fadi gaskiya. Kuna bukatan fadin dukkan abubuwar raunata da suka yi muku. Ku gaya musu baza ku iya cigabawa da abokantakar kuma ba. Ku guje shafa musu laifi. Mai yiwuwa kuma kuna da laifi. Banda yin ihu ko fada dan Allah. Kuma banda zagi. Idan kuna jin tsoro, zaku iya yin gwaji a gaban madubi.

Ku tura musu sakon rubutu
Wasu lokuta yana da kyau a rubuta abubuwa a maimakon fadin su da baki. Saboda haka, ku tura wa “Kawar” nan wani sakon rubutu. Zai taimake ku bayyana abun dake ran ku da kyau.
Kuma, zamu iya ganin kalmomi masu laifuffuka kuma mu cire su. ya kamata a bi da rabuwa da hankali.

Kada ku fadi abubuwa mara kyau akan su
Idan abokantakar ya kare, labarin zai baje da sauri. Yan fitina zasu so su kokarin saka ku falasa sirrin abokan mu na da. Zasu zo da kowane irin labarai saboda su saka ku yin magana. Amma kada ku fada wa irin dabaran su.

Kada kuyi dana sani
Yawancin abokantaka na taimakon mu zama mutane mafi kyau. Shiyasa bai kamata mu bawa kan mu laifi dan mun kasance a daya. Duk yana cikin rayuwa. Muna girma, muna koyo, kuma muna fuskanta gaba. Duk da haka, mu ajiye wannan masaniyar a cikin zuciya, saboda kada ya kara faruwa kuma.

Kun taba samun wata abokiya mai guba? Ya kuka rabu dasu? Gaya mana!

Share your feedback