Mayar da abun da na koya

“ Wanda aka bawa abu mai yawa, ana sa ran zai maida da yawa”

Idan wani ya taimaka ya inganta rayuwar mu, yakamata mu ma muyi kokarin taimakon wasu. Idan muna da hankali da kuma kyauta, zamu iya inganta duniyar mu.

Abun farkon daya kamata mu fara yi shine mu gaya wa sauran yan mata akan Springster. Ku rarraba abubuwa masu muhimmanci da kuka koya. Su san yadda abubuwan da kuka koya daga nan ya taimake ku.

Wasu yan mata sun fara rarraba labarai akan yadda suka gaya wa sauran ‘yan mata akan labaran Springster. Yawancin ‘yan matan nan sun koya sabobin kwarewa, da hanyoyi mafi kyau da zasu yi wa mutane magana, da sidabbarun tsirata kan su da kuma abubuwa fiye da haka. Ga wasu misalai a nan kasa;

‘Yar uwa ta ta gaya mu akan Springster. Ina son labarin nan akan wata yarinya da ta fara kasuwancin yin dinki saboda ina son na koya dinki. Na koya wasu darussa kuma ina sa rai cewa zan je makarantar zane idan na kara girma. Esther, shekaru goma sha uku

Abokiya ta bata tabbata ko ta karbi kyauta daga wajan wani tsohon mutum. Na tura mata wani makala akan karban kyauta daga masu daukan nauyi dana gani a Springster. Da ta karanta, ta yanke shawara cewa baza ta karba kyautan ba. Wannan makalar ya taimake ta yanke shawara cewa yawancin mutane zasu so su karbi wani abu daga wajan ta. Bata son wannan ya faru. Amina, shekaru goma sha biyar

Ina da abokiya dake da damuwa akan samun warin nunfashi. Dana ga wani makala a Springster mai lakanin “Yadda na bi da warin nunfashi”, nan take na tura mata. Ta gaya mun yadda take ta amfani da lemun tsami da kuma gishiri. Ya taimake ta sosai. Mahaifiyar ta ma ta lura cewa nunfashin ta na kamshi kwanakin nan. Tega, shekaru goma sha bakwai

‘Yar uwa ta nata naiman shafin yanar gizo gizo dake da bayanai wa ‘yan mata tsaran ta. Ranar dana ga wannan shafin a samar Free Basics, na kira ta ta karanta makalar kuma ta so hotunan yan mata kamar ita kuma da karanta labaran yan matan. Bayo, shekaru goma sha bakwai

Rarraba misalai yadda kika rarraba abubuwan da kika koya daga Springster ko kuwa daga wasu wajaje a sashin sharhin a nan kasa.

Share your feedback