Na san cewa jira ne mafi kyau ga ni

Tiwa nada babban tambayoyi akan daukan soyayyar ta zuwa mataki na gaba...

Tiwa mai shekaru goma sha bakwai, na fita da Bayo mai shekaru ishirin da daya dake zama a ungwan su na watani bakwai.

Kwannan nan Bayo nata tambayar ta su dauke soyayyar su zuwa mataki na gaba. Yace mata idan tayi, zai nuna cewa tana kaunar sa.

Wannan ya rikitar da Tiwa. Tayi wa abokan ta magana akan sa. Bisa ga abokan ta, yawanci yan mata sun gwada.

A mako daya wuce Tiwa ta ziyarta yar uwar ta likita. Ta gaya mata akan saurayin ta. Kuma ta gaya mata abun da abokan ta suka fada.

Duk da yake tana son ta jira, amma duk da haka bata son ta bata wa saurayin ta rai. Kuma tana son ta zama kamar abokan ta da suka gwada.

Yar uwar Tiwa ta bata shawara akan abun yi

Tiwa, idan yazo akan soyayya baki bukatan yin jima’i domin nuna kauna. Idan kina bukatan daukan soyayyar ku zuwa mataki na gaba, yakamata ki tambaye kanki ko kin shirya. Yin jima’i na zuwa da sakamako. Zaki iya daukan ciki. Kuma zaki iya kwashen cuta.

Idan ke da saurayin ki naji kamar kuna bukatan daukan soyayyar ku zuwa mataki na gaba. Yakamata ki kare kanki. Ina nufin cewa, kuyi amfani da kwaroron roba. Kuma yakamata ku tattauna abun yi idan kika dauka ciki.

Zan baki shawara ki zo asibiti na (Kizo tare da shi) domin muyi magana akan ra’ayin ki da kuma baki maganin hana haihuwa. Idan kina jin kunyar zuwa asibiti na, ku nemo wani cibiyar lafiya da zai iya taimakon ku.

Amma duk da haka, idan kina ji kamar baki shirya yin dukkan abun dana fadi ba, toh mai yiwuwa baki shirya wa mataki na gaba ba. Kina da isashshen lokacin yin shiri a nan gaba.


Duk da yake na sassauta bayan dana yi magana da yar uwa ta amma ina dan jin tsoro akan yadda zan gaya wa saurayi na ya yarda mu bi shawarar yar uwa ta.

Na gaya wa yar uwa ta akan damuwa na.

Tace:

Tiwa kada ki bari saurayin ki ya matsa miki lamba. Ke zaki yanke shawara akan abun yi. Idan baki shirya ba kuma ya cigaba da matsa miki, mai yiwuwa ba shi bane saurayi mafi kyau miki. Wanda yake kaunar ki zai girmama ra’ayin ki. Kuma ki tuna idan ya tilasta ki yin wani abun da baki so, ki kawo rahoton sa a waje na ko mahaifiyar ki nan take.

Kuna da wani kamar yar uwar Tiwa da zaku iya yin wa magana akan komai? Gaya mana akan mutumin a wajan sharhi.

Share your feedback