Ya mun tsufa?

Amsar da baku sani kuna nema ba

Sannu Babban Yaya,

Ban san daga inda zan fara ba. Akwai wani saurayi da nake so dake da sunnan Jude. Yana da hankali. Zan iya gaya masa komai. Babu kamar irin sa. Ya hadu. Akwai sanda ya kai ni wajan shan kankarar farari. Da kun ga yadda sauran yan mata suka saka mana ido! Nayi alfaharin kasancewa dashi.

Yau ya tambaye ni na zama budurwar sa. Zanyi ihu nace ‘Eh” sai nayi fargaba. Shekarun sa ishirin da hudu ni kuma shekaru na goma sha shida!! Bana son abokan sa su kira ni jaririya. Kuma ina tsoron abun da sauran mutane zasu ce. Wasun su zasu yi tunanin ko ina bin sa domin kudin sa ne.

Tunda ya girme ni sosai, ina tsoron zai so yayi wasu abubuwa da ban shirya yi ba. Kuma bana son nayi asarar sa domin wannan.

Ina son sa sosai! Baya da yaranta kamar samari tsara na. Yana da kama kai. Ban san abun yi ba. Babban yaya, ki taimake ni!

Nagode,
Kate (ba asalin suna na bane)


Sannu Kate (ba asalin suna na bane), 

Ayyah! Ba komai, yarinya. Naga dalilin daya sa kike son Jude. Amma da yake ya girme ki, abubuwa zasu dan yi wuya. Yaruwar ku dabam ne, saboda haka yana da kyau ku tabbata cewa kuna son abubuwa daya. Misali, idan kuna son irin wakoki daya, zaku samu abun yin magana akai.

Wasu lokuta samari masu shekaru dayawa zasu so su fita da kananan yan mata domin suyi iko dasu. Saboda haka ki lura da wadannan alamun.

Yana yawan gaya miki abun da zaki yi? Karbe ki a yadda kike? Girmama ra’ayin ki? Ki ajiye wadannan a zuciya. Ta nan, baza ki kasance da wani dake bi dake kamar jaririya ba. Saboda idan yayi haka, abokan sa ma zasu yi.

Kuma, mai yiwuwa Jude ya shirya yin soyayya mai muhimmanci. Mai yiwuwa ya so ya kai soyayyar zuwa mataki na gaba. Kada a matsa miki yin abun da baki shirya yi ba.

Sai ki tambaye kanki: Ina son shi da gaske, ko dai ina son sa domin shekarun sa? Zai taimaka idan kin tabbata. Domin ki kasance dashi dan dalilai masu kyau.

Ki tuna ki duba ko yana yin soyayya da kananan yan mata ne kawai. Idan yana haka, ba al’amari mai kyau miki bane ko wata dabam.

Ina fatan wannan ya taimaka. Allah bada sa’a!

Da kauna
Babban Yaya (asalin suna na)

Share your feedback