Yana da kyau na samu wani da zai dauka nauyi na?

Dalilin daya sanya cewa amshan kudade da kyauta daga tsofofin maza bai da kyau

Wasun mu na iya sanin wasu mata masu maza dake daukan nauyin su. Tsofofin maza dake basu kudi da kuma kyauta. Daga shafin dubawan ki zaki ga kaman irin matan nan na jin dadin rayuwan su. Ama baza ki iya sanin asalin labarin su ba.

Ki kiyaye amshan kudi da kyauta. Mutumin zai iya son wani abu daga wajan ki.

  • Zai iya matsa lamban ki akan jima’i
  • Zai iya tilasa ki yin wani abu mai tattare da kasada
  • Zai iya iko dake yace zai daina baki kyauta idan baki aikata abun da yace ba

Idan kika cigaba da dogara dashi domin kudi da kyauta, zai kara karfin iko a rayuwan ki.

Ba ko wanda tsohon namiji daya baki kyauta bane ya tsara zai miki lahani. Ga misali, kawun Aisha na biyan mata kudin makaranta. Yana bawa mahaifiyar Aisha kudi. Baya tambayanta ta bashi komai ko ya sata jin wani iri.

Idan wani tosohon namiji yace zai baki kyauta ko yace yana son ya taimake ki, ki gaya wa wata babba da kika sani. Idan mutumin baida aniya maras kyau, ba zai damu ba. Idan mutumin yace miki kada ki gaya wa kowa, toh ki kiyaye. Kada ki sake ki hadu dashi ke daya.

Ki tabbata kin rarraba wannan abun da abokai ki saboda suma su tsare kansu.

Share your feedback