mama wannan kauna ne?

Ki koya yin magana idan aka raunata ki

Salam Mama,

Ina kallon abokai na da mahaifansu. Basu yi kaman yadda mukeyi. Ance ko wanda uwa na kaunan yaran ta. Kauna ne idan kika mun duka da zagi?

Ina da tabo daga dukan da kika mun da cokalin itace saboda na kara gishiri da yawwa a cikin shinkafa. Kamar kina duka ne ko wanda lokaci. Kina kira na mara sauri, sakara, mara amfani. kina yawan gaya mun ba zan samu nasara ba a yadda nake tafiya da rayuwa. Abokai na basu jin tsoron mahaifiyarsu. ba yadda nake tsoron ki ba. Suna magana da mahaifiyarsu ba tare da tsoro ba. Ban iyawa saboda kina yawwan cewa ina tambayen kuruciya. Kina fadi wai kina bi dani haka saboda baki son na lalace. Kina fadi wai kina horar dani saboda kina kauna na. . Yar uwa tace ana kiran abun da kike mun cin zarafi na baki dana duka. Tace bai kamata a bida mutum haka ba. Tace ki bi da mutane da kike kauna da hankali.

Mama tana da gaskiya? ko dai kauna da kike mun yafi nata?

Mama wannan kauna ne? idan na haifa nawa yaran, haka zan bi dasu? Ban tsammani ba. Zan gyara su a mutunce.

Ina addu’a wannan wasikan zai taimaka ya nuna miki yadda nake ji. Ina addu’a zai bani saukin samun yin magana dake

Tare da kauna, Diyar ki.

Kina cikin halin nan ko kin san wata dake cikin halin nan? Dan Allah kiyi wa wata da kika yarda da magana akan irin abun nan, kada kiyi shiru. Zaki iya mana magana a shafin sharhi.

Karanta ANA BI DA KE YADDA BAI KAMATA BA?

Share your feedback