Safga na ya canza rayuwana

Lokaci ya kai da za’a dauki mataki

Da iyaye na suka rasu, na zata rayuwana ya kare. Ni kadai suka haifa, kuma su ne gaba dayan rayuwana. Na zama ni daya babu jagoranci ko goyon baya na kwarai - musamman idan yazo akan yanke shawara.

Sai Inna na da kawu na suka dauke ni. Suna lura dani kamar ni yar su ce. Ina godiyar alherin da suke mun, amma ina jin bakin ciki akan dogara akan su wa komai. Yana saka ni jin wani iri, musamman dayake suna da nasu yaran da suke lura da. Bana son na daura musu nauyi.

Wani rana, abokiyata Agianpe ta zo ziyarta ni. Muka dan yin labari, sai nayi mata kitso a bayan gidan mu. Ina son yin kitso da kuma gwada tsarin gashi dabam.

Bayan da Agianpe ta tafi, Inna na ta bani shawara na fara samun kudi daga safga na. Na dan yi mamaki. Ban san cewa ta san abun da nake son yi ba. Ashe ta gane yadda nake ji kuma tana son ta taimake ni

Kafan nan, ban taba tsammanin zan iya samun kudi daga yin abun da nake so ba. Na kosa na fara.

Inna na ta taimake ni sosai. Ta bani wani dan fili a gida na riga yin kitson. Har ta bari nayi kwaji da gashin yan uwa na. Da makwaftar mu suka yi sha’awar gashin su, Inna na ta sanar musu cewa ni na musu kitson. Kai na sai kara kato yake tayi.

Da wasa da wasa, na fara samun abokan kasuwanci. Da lokaci ya dan wuce, suka fara karuwa. Bada jimawa ba ina cike da aiki a karshen mako. Kafan na sani, ina daya daga cikin sannanun masu kitso a al’ummar mu..

Tun sanda na fara sana’a na, na kara tabbaci da kai na. Bana damuwa da rayuwana na gaba kuma- saboda ina da nawa kudin. Ina ji dama iyaye na na nan su gan ni yanzu. Zasu yi alfahari dani.

Mu kama aiki yan Springster! Wanne safgar ku ne zaku iya juya zuwa sana’a? Ku gaya mana a nan kasa.

Share your feedback