Abokantaka a cikin dadi ko a cikin wahala

Dabaru akan yadda zaku zabi abokan arziki

Tunanin ku (3)

A rayuwa mutane zasu zo kuma su tafi. Amma abokan arziki zasu tsaya daku.

Zaku iya yin musu magana akan komai. Zasu lura daku.

Zaku iya nuna asalin kanku idan kuna tare dasu.

Abokan arziki zasu taimake ku a duk hanyar da zasu iya. Baza su raina ku ba.

Suna gaya muku gaskiya.

Wadannan ne “abokan ku na cikin dadi da cikin wahala”. Yana nufin cewa zasu goya muku baya koda menene.

Kuna da abokai kamar haka ko kuna kokarin neman su? Ga wasu hanyoyi da zaku gano abokan cikin dadi da wahala

  • Mutane ne dake da dabi’u daya daku. Ba lailai sai kun so abubuwa iri daya ba. Amma daraja abubuwa iri daya kamar kasancewa mara karya ko kuwa taimakon sauran mutane zai jawo ku kusa. Kuma idan kuna son irin wakoki daya ko wasan kwakwaiyo daya zaku samu abun tadi koda yaushe.
  • Abokan arziki na imani da ku. Abokan cikin dadi da wahala baza su raina ku ba.
  • Wasu ne da zasu baku lokacin su idan kuna bukatan su. Abokai ne da zaku iya yarda da.
  • Abokan arziki mutane ne da zaku iya walwala da. Ba sai kun wayince kafan su so ku ba. Abokan arziki zasu so ku a yadda kuke.
  • Kuna bukatan wani da zaku yarda da, wata da ba za ta fada wa sirrin ku da duniya. Idan kuna son abokan cikin dadi da wahala yakamata ku ma ku zama haka.

Kuna kokarin samun abokai? Kada kuji kunya. Ku gabato wata da kuke so a makaranta ko kuwa wata makwaftar ku. Ku fara yin magana dasu. Ku tambaye su akan ranar su. Kuyi musu tayin wani abun ciye-ciye. Ku yabe yadda suke amsa tambayoyi a aji. Ku fara tattaunawa akan wakoki da kuke so ko kuwa wasan kwakwaiyo da kuke kallo.

Ya kuke samun abokai? Ku rarraba dabarun a nan kasa a wajan sharhi

Share your feedback

Tunanin ku

yayi kyau

March 20, 2022, 7:55 p.m.

Latest Reply

sannu marys ya kike?

Sannu yarinya! An rubuta wannan makalan saboda ke ne kuma muna farin ciki cewa kina son shi. zaki iya rarraba da abokai ki.