Fadi abun da kike so, yarinya!

Ku fadi abun dake ran ku da karfi da alfahari

Kun tuna wani lokaci da kuka yi magana akan wani abu da kuke so? Ya kuka ji? Dadi, ko? Kun ga, wa mu yan mata, muryan mu shine babban makamin mu. Idan muka koya yin magana, zama samu girmamawan nan da muke cancanci. Zamu nuna asalin kanmu.

Idan wani ya kira ku sunaye, kuce ya “daina”. Ku gaya musu abun da suke yi bai da kyau. Kuyi kokari kada kuyi amfani da kalmomi zagi. Kuyi magana da mutunci.

Idan abokan ku suka baku haushi, kada kuyi kamar bai dame ku ba. Ku tuna, baza su iya karanta zuciyar ku ba. Ku gaya musu yadda kuke ji. Idan baza ku iya gaya wa mutum gaskiya ba, toh abokantakan bata da amfani.

Yanzu kuyi tunanin wannan. Kuna kasuwa da mahaifiyar ku. Tana son tayi muku kyauta. Tace ku zabi tsakanin wani riga ko kuwa wannan sassakan katakon nan da kuke so. Kuna tsoro idan kuka dauka sassakan katakon nan mutane zasu kale ku da wani irin ido. Amma ga gaskiyar: Mutane zasu yi magana koda menene kuka fada ko kuka yi. Saboda haka, kuyi abun da kuke so.

Kuma, idan wani yaro yace yana son ku, ba dole bane sai kun yarda. Kada ku wayince kamar kuna son sa kawai domin ku saka shi jin dadi. Kawai kuce a’a, kuma idan ya cigaba da matsa muku, kuyi magana da wani amintaccen babban mutum akan sa.

Idan kuka yanke shawara lokacin da kuka shirya zama fiye da abokai da namijin da kuke so, yin magana nada muhimmanci. Yan da sauki ku bar wani yayi abun ganin damar sa saboda kuna son su. Amma wannan zai iya saka ku cikin matsala. Saboda haka ku gaya musu yadda kuke so a bi da ku. Idan mutumin da kuke gani na muku magana da rashin mutunci, kuce “baku son haka”. Idan suka kirashe yin wani abu da baku so, kuyi magana akan sa a nan take. Idan suka ki suji, ku kai rahoto a wajan wani amintaccen babban mutum.

Amma duk da haka, fitowa da abun dake zuciyar ku bai da sauki. Kuna damuwa mutane baza su so ku ba. Amma hanyar da zaku walwala shine idan kuka fadi gaskiya. Idan kuka wayince ku zama wani daban baza ku samu abun da kuke so na asali ba. Kuma mai yiwuwa wannan zai saka ku bakin ciki.

Kuma ku tuna cewa duniya babban waje ne. Wani zai so ku yadda kuke. Saboda haka kuyi magana kuma kuyi tafiya da kan ku a tsaye. Jeki yarinya.

So nawa kike fadin zuciyar ki? So daya a wani lokaci? Koda yaushe? Zamu so mu sani. Gaya mana a nan kasa.

Share your feedback